Fiye da mutane miliyan 26 ne ke bukatar agajin jinkai a fadin kasar, a cewar hukumar IOM. / Hoto: AFP

Hare-haren kungiyoyin ta’addaci a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, DRC, kan fararen-hula sun karu, lamarin da ya raba mutane kusan miliyan daya da muhallansu tun daga farkon shekarar 2023.

Kimanin mutum miliyan 6.1 ne suka rasa matsugunansu a kasar, karin kusan kashi 17 cikin 100 da aka samu daga Oktoban 2022, a cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, IOM, a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

"Yawaitar hare-hare kan fararen-hula na kungiyoyi masu dauke da makamai ta sa mutane kusan miliyan daya sun rasa matsugunansu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo tun daga watan Janairu.

"Yayin da rikicin kasar ke kara ta'azzara, al'amuran jinkai na ci gaba da tabarbarewa, kuma miliyoyin mutane na fuskantar matsalar karancin abinci da muhimman bukatu," a cewar sanarwar

Hukumar ta bayyana cewa akalla mutane 46 ciki har da kananan yara aka kashe a wani hari da ‘yan kungiyar hadaka ta ci-gaban Kongo CODECO suka kai a yankin Lala da ke lardin Ituri ranar 11 ga watan Yuni.

Harin ya yi sanadin raba mutane sama da 7,800 da kuma asarar gidaje da kayayyakin jama'a.

Hukumar ta IOM ta yi tir da wannan “mummunan keta haddi” na dokokin jinkai na kasa da kasa, ta kuma ce hare-hare kan fararen-hula na iya zama laifuka na yaki.

"Wannan mummunan hari na baya-bayan nan shaida ce ga irin hadurran da ke sa mutanen da ke gudun hijira a DRC ba ba za su iya jurewa ba", In ji Federico Soda, daraktan Sashen Gaggawa na hukumar IOM.

"Ana matukar bukatar a yi kokarin kawo karshen wannan tashin hankali da kuma taimaka wa al'ummar Kongo wajen samun zaman lafiya," a cewar Soda.

Fiye da kungiyoyi 120 masu dauke da makamai ke aiki a kasar

Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun yadu sosai a yankin Gabashin DRC kusan tsawon shekaru talatin kenan, yakin da ya zama gado tun da ya barke a shekarun 1990 da 2000.

Kungiyar M23 da Tutsi ke jagoranta ta kwace yankuna da dama a lardin Kivu na Arewa tun bayan da ta dauki makamai a karshen 2021 bayan lafawar da ta yi na tsawon shekaru.

DRC ta zargi Rwanda da mara wa kungiyar M23 baya.

Duk da rashin amincewar Kigali, kwararrun Majalisar Dinkin Duniya masu zaman kansu da wasu kasashen Yammacin Duniya, ciki har da Amurka, sun amince da Kinshasa.

Yankin dai na da kungiyoyi masu dauke da makamai sama da 120, wadanda galibinsu ke fafutukar neman filaye da sarrafa ma'adanai masu daraja, wasu kuma na kokarin kare al'ummominsu.

Sama da mutane miliyan 26 ne ke bukatar agajin jinkai a fadin kasar, a cewar Hukumar IOM.

TRT World