Fararen-hula akalla 13 ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin kungiyar ta'addanci mai alaka da Daesh ta kai a arewacin Mali, kamar yadda wasu jami'ai da ba sa so a ambaci sunansu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Mutum 13 ne suka mutu, gommai kuma suka jikkata sannan daruruwa sun tsere daga kayukansu da ke yankin Gabero" a lardin Gao, a cewar wani jami'i , yana mai karawa da cewa sojojin Mali ba sa yankin da lamarin ya faru ranar Laraba.
"Sun kashe mutane da dama, fiye da mutum 17," kamar yadda wani jami'in na Gao ya yi ikirari.
"Dukkan matasan yankin sun gudu. Yawancin lokuta maharan suna satar dabbobi. Wannan ne karon farko da suka kashe mutane da yawa kamar haka," in ji shi.
'Yan ta'addan sun fi mayar da hankali wajen kai hari a Gao da Menaka da ke gabashin Gabero tun farkon shekarar 2022.
Irin wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar dubban fararen-hula sannan suka sanya mutane tserewa daga gidajensu zuwa sansanonin 'yan gudun hijira, da kuma tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka.
Rashin tsaro ya yi kamari a kasar tun bayan da kungiyoyin da ke da alaka da Daesh da kuma masu neman ballewa daga kasar suka kaddamar da hare-hare kan gwamnati da fararen-hula a arewacin kasar a 2012.