Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai a wani wurin hakar ma’adinai na Tabarkat da ke arewa maso gabashin Arlit.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Nijar din ta fitar, ta ce maharan sun isa wurin hakar ma’adinan ne a cikin motoci takwas.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun isa wurin da wuri wanda hakan ya sa suka dakile harin kuma suka kora maharan zuwa arewacin kasar.
Sojojin sun ce suna ci gaba da bi domin neman maharan. Sojojin sun ce a yayin dakile harin, sun kashe har mutum uku daga cikin maharan kuma sun kwato motoci kirar Toyota guda hudu har da wadda ta kone.
Sai dai maharan sun lalata motar sojin guda daya ita ma kirar Toyota.
Sojojin kuma sun ce sun kwato bindiga mai sarrafa kanta da makaman roka da dama da harsasan su.
Shugaban sojojin Nijar Abdou Sidikou Issa ya jinjina wa sojin kasar da kuma kara masu kwarin gwiwa kan kare kasa.
Ana yawan samun hare-hare na ‘yan bindiga da kuma masu ikirarin jihadi a Jamhuriyyar Nijar.
Ko a kwanakin baya sai da ‘yan bindigar suka kashe sojoji biyar a yankin da ake hakar gwal kusa da Aljeriya a cikin Nijar din.
Sa’annan kuma a watan Mayu sojojin kasar bakwai nakiya ta kashe a yankin Tillaberi, wanda yanki ne da ake fama da rashin tsaro a kasar.