Hukumomi da ganau sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kashe kusan mutum dari a hare-haren da suka kai a jihohin Sokoto da Zamfara da Binuwai da ke Nijeriya.
Kazalika an sace gomman mutane, ciki har da mata.
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kashe akalla mutum 30 a harin da 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Tangaza a karshen mako.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Ahmad Rufai, ya fitar ranar Lahadi ta ce 'yan bindiga sun kai hari a kauyukan Raka, Bilingawa, Raka Dutse, Jaba, Dabagi da Tsalewa ranar Asabar.
Sanarwar ta kara da cewa kafin kai harin, wasu 'yan kato-da-gora sun je kauyen Azam inda suka gargadi jama'a.
“Sai dai yayin gargadin, 'yan kato-da-gorar sun wuce gona-da-iri inda suka rika dukan mutanen kauyen wadanda galibinsu Fulani ne.
“Hakan ne ya sa 'yan kauyen suka bukaci agaji, kuma abin takaici taimakon ya zo ne daga wurin 'yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne wadanda suka je a kan babura 20," in ji ASP Rufai.
Ya ce 'yan kato-da-gorar sun janye daga kauyen bayan sun gano cewa 'yan bindiga na kan hanyar zuwa wurinsu, yana mai cewa 'yan bindigar sun bi 'yan kato-da-gorar kuma sun kashe takwas a Raka, bakwai a Bilingawa, shida a Jaba, hudu a Dabagi, uku a Raka Dutse da kuma biyu a Tsalewa.
Kazalika kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar da kai hari a wasu kauyukan karamar hukumar Gwadabawa, ko da yake bai bayyana adadin mutanen da aka kashe ba. Sai dai ganau sun ce an kashe mutane da dama.
An sace mutane a Zamfara
Hare-haren na Sokoto na faruwa ne a yayin da a Zamfara da ke makwabtaka, wasu 'yan bindiga suka kai hari a kauyukan Janbako da Sakkida ranar Asabar inda suka kashe akalla mutum 24.
'Yan bindigar sun sace 'yan mata sama da 30 da suka je yin itace a kauyen Gora sannan suka kashe mutane da dama a kauyen Janbako.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara Yazid Abubakar ya tabbatar da kai harin, sai dai ya ce mutum 13 aka kashe sannan aka sace kananan yara maza da mata guda tara.
Ya ce ana ci gaba da bibiyar 'yan bindigar da zummar kwato wadanda aka sace, amma rahotanni sun ce tuni tara daga cikinsu suka koma gida.
Amma Hussaini Ahmadu da Abubakar Maradun, mazauna kauyukan Janbako da Sakkida, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa tun da fari 'yan bindigar sun bukaci mazauna kauyukan su biya su kudi kafi su bari su yi noma, amma ba su biya ba.
A jihar Binuwai da ke tsakiyar kasar, 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 25 sannan suka cinna wa gidajensu wuta a harin da suka kai ranar Asabar a kauyen Imande Mbakange, a cewar wasu ganau.
Kawo yanzu ba a san dalilin kai harin ba, sai dai an dade ana rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Binuwai.
'Yan sanda ba su amsa kiraye-kirayen da aka yi musu kan batun ba.