Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar wasu karin yaran su mutu zuwa karshen shekara. Hoto/Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara fiye da 1,200 ne suka rasu a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Sudan tun daga watan Mayu.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar ce ta bayyana hakan a ranar Talata inda ta yi gargadin cewa akwai wasu dubbai da ke sansanonin wadanda za su iya mutuwa zuwa karshen shekara a kasar da yaki ya daidaita.

“Sama da yara ‘yan gudun hijira 1,200 'yan kasa da shekara biyar ne suka rasu a sansanoni tara tsakanin 15 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Satumba,” in ji Allen Maina, shugaban kiwon lafiya na Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Mista Maina ya ce yaran sun rasu ne bisa zargin barkewar cutar kyanda da kuma rashin samun isasshen abinci.

Tun bayan barkewar yaki a Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin shugaban sojojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo, kusan mutum 7,500 aka yi kiyasin an kashe.

Haka kuma wannan yakin ya sa sama da mutum miliyan biyar sun rasa muhallansu, daga ciki har da mutum miliyan 2.8 wadanda suka tsere saboda hare-hare ta sama da ake ci gaba da kai wa, da harbe-harben makaman atilari.

AFP