Daga Coletta Wanjohi
A kowace safiya a shirinta na rediyo, mai gabatarwa Salma Msangi na magana kan batutuwa da suka shafi uwa, inda take yawan kawo misali da kanta wurin renon jariri.
Masu sauraren rediyo a Tanzania suna sane da mahangar Salma kan batun shayar da nonon uwa zalla ga jarirai, lamarin da take yawan wayar da kan iyaye wadanda suke da shakka wurin shayar da 'ya'yansu.
“A lokacin da na hafi jaririna na farko, na fuskanci kalubale wurin shayar da nono,” kamar yadda Salma ta shaida wa TRT Afrika.
A matsayinta na sabuwar uwa, takan cika da shakka idan danginta suka ce mata bai wa jaririnta ruwan nono kadai yana hana shi samun sauran sinadarai.
“Hakan ya sa nake neman agaji daga asibitin da na haihu,” in ji ta. “Kwararru na asibiti na yawan taimakona, inda suka sa na gano cewa ruwan nonon uwa zalla ya ishi jariri a watanni shidansa na farko.”
Wannan ba wai batu ba ne kawai na birni. A wani kauye da ke Yammacin Kenya, Sarah Khatievi na tare da jikokinta shida wadanda suka je kai mata ziyara.
Dattijuwar mai shekara 68 ta tuna cewa duka ‘ya’yanta takwas, ta rinka hada musu da abinci mai nauyi a lokacin da take shayar da su.
“Jariri ba zai iya rayuwa da ruwan nono kadai ba – wannan shi ne abin da iyayenmu suka koya mana,” in ji Sarah.
“Ga duka ‘ya’yana, ina dan kara musu ruwa a abincinsu da kuma ruwan nono. A lokacin da za su yi wata biyar haka, ina soma ba su dankali mai laushi da kuma fate kafin na yaye su baki daya daga ruwan nono bayan watanni shida.”
Sarah ta yi dariya da karfi a daidai lokacin da ta shaida wa TRT Afrika wata tatsuniya ta matan zamanin baya wadda ita ma aka ba ta.
Mahaifiyarta ta shaida mata cewa idan wani yana son ya san cewa yaro ya ci ya koshi, sirrin shi ne mutum ya yi ta duba cikin jaririn a lokacin da yake cin abinci. “Idan ya yi kamar kwallo, wata alama ce ta cewa jaririn ya koshi.”
Abincin iri daya
Shayar da nonon uwa zalla na nufin abin da kawai zai iya shiga cikin jinjiri shi ne ruwan nonon mahaifiyarsa. Ko digon ruwa ba za a ba jariri ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta bayar da shawarar cewa a rinka bai wa ko wane jariri nonon uwa zalla, domin yana dauke da sinadarai masu gina jiki wadanda za su taimaka wa cikinsa zuwa akalla watanni shida na farko bayan haihuwarsa.
Hukumar ta kuma bayar da shawara ga iyaye mata da su soma bai wa jariri nono za zarar an haife shi kafin ya kai awa daya, duk da hakan wani kalubale ne ga mata da yawa.
“Wasu iyaye mata suna damuwa cewa ba su da isasshen ruwan nonon da za su shayar da jariransu,” in ji Victoria Kirway, wata malamar jinya da ta kware kan kula da jarirai sabbin haihuwa a asibitin CCBRT da ke birnin Dar es Salaam na Tanzania.
“Muna yawan cewa mai yiwuwa hakan na faruwa ne sakamakon matsalolin da ake samu sakamakon sauyin sinadaran jiki, amma daga baya ana samun ruwan nonon.”
Victoria ta ce mahaifiya ba ta bukatar ta rinka damuwa da batun samar da ruwan nono mai yawa, inda take tabbatar da cewa ruwan nonon zai rinka zuwa a hankali.
“Idan aka haifi yaro, ba ya bukatar wannan madarar; abin da jariri ke bukata ta hanyar shayarwa ya isa. Kawai ka sa yaro ya rinka tsotso bayan awa biyu zuwa uku, ruwan nonon zai ta karuwa.”
Shayar da nono da kyawun ‘ya mace
A duk lokacin da take tattaunawa da mata sabbin haihuwa a shirinta na rediyo, Salma na cin karo da batutuwa game da shayar da nono da kuma kyawun ‘ya mace.
“Daga ina kuke saurarenmu? Ki gaya mana dalilin da ya sa ba kya shayar da nono,” ana yawan jin ta a bangare na biyu na shirin tana saka wata waka ta Swahili wadda ke magana kan mata da kuma kyawun su.
Wannan bangaren yana da farin jini kuma yana jawo masu kiran waya da dama, musamman mata matasa wadanda suke yawan cewa ba sa shayar da nono saboda suna so su ci gaba da zama masu kyau.
“Mutane na yawan son magana kan wannan lamarin; batun ba ya tsufa,” kamar yadda Salma ta shaida wa TRT Afrika.
“Matasan mata da dama sun yi ammanar cewa idan suka shayar da nono, girma da yanayin nononsu zai sauya,” in ji wata mahaifiya mai ‘ya’ya uku.
“Abin da ‘yan uwana mata ba su gane ba shi ne girma da yanayin nono yanayin halittar mutum ke mayar da shi yadda yake ba shayar da nono ba.”
WHO da UNICEF sun bayyana cewa “jariran da ba sa shan nono sun fi hatsarin saurin mutuwa sau 14 kafin su cika shekara daya da haihuwa fiye da wadanda aka bai wa nonon uwa zalla”.
“Muna da iyaye mata da ke zuwa da ‘ya’ya marasa lafiya kuma idan muka yi bincike, suna shaida mana cewa ba su taba ba jariransu nono ba. Idan muka kara bincike, sai mu ga wadannan iyayen ba su da wata hujja ta kin bai wa ‘ya’yan nasu ruwan nono,” in ji malamar jinya Victoria.
Kamar yadda likitoci suka bayyana, yaron da aka bai wa nonon uwa zalla a watannin farko bayan haihuwarsa ya fi saurin girma da kuma samun kaifin basira.
“Muna yawan shaida wa wadannan iyayen mata cewa idan suka hana ‘ya’yansu ruwan nono, suna kokarin karya musu garkuwar jiki wadda ke kare su daga cututtuka.
Shayar da nono zai iya kare yaro daga cutar namoniya da sankarau da cutar mafitsara da asma da ciwon suga da cutar kiba da kuma ciwon zuciya,” in ji Victoria.
Haka kuma bayar da nonon shi ma yana taimaka wa iyaye mata inda yake kare su daga cutar kansa ta mahaifa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa an samu karuwar shayar da nonon uwa zalla a kasashen Afirka kamar su Côte d'Ivoire da Somalia sakamakon irin wayar da kai da ake yawan yi kan amfaninsa.
Shayar da nonon uwa da aiki
Bukatar komawa aiki bayan an haifi jariri da kuma karancin wuraren shayarwa a wuraren aiki wani kalubale ne ga iyaye mata wadanda suke son ci gaba da shayar da nonon uwa zalla, amma ba za su iya yin haka ba saboda dalilai na kai da kuma asibiti.
A kan haka ne ake makon shayar da nonon uwa na duniya daga 1 zuwa 7 ga watan Agustan kowace shekara, ke kara samun muhimmanci.
A bana, taken ranar shi ne “Mu sa shayar da nonon uwa a wurin aiki ya yi aiki”. WHO na bukatar duka ma’akata da su goyi bayan shayar da nono uwa a wuraren ayyuka.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da UNICEF, ta bukaci wuraren aiki da masu daukar aiki da su rinka bayar da “isashen hutu ga duka iyaye ma’aikata da masu kula da yara domin biyan bukatun ‘ya’yansu.”
Wadannan sun hada da hutun haihuwa tare da biyan su albashi na akalla makonni 18, idan da so samu ne tsawon watanni shida ko fiye da haka bayan haihuwa.