Ma’aikatar abinci da aikin gona ta Ghana ta cire takunkumin da ta saka kan jigila da yankawa da cin dabbobi da jakuna a gundumar Binduri da ke yankin Upper East na kasar.
A ranar 31 ga watan Mayun 2023 ne gwamnatin kasar ta haramta yanka dabbobi da cin nama a gundumar bayan bullar cutar anthrax, wadda dabbobi kan iya saka wa bil adama.
A sanarwar da ma’aikatar ta fitar a ranar Talata, ta ce an shawo kan matsalar kuma ba a sake samun wannan cuta ta anthrax ba tun 14 ga watan Yuni.
Sai dai hukumar ta ce ko da yake an dage takunkumi kan cin naman dabbobin da jigilarsu, duk da haka akwai ka’idoji da ta gindaya da suka kamata a bi domin kara kiyayewa.
- Dole ne likitan dabbobi da jami’an kula da muhalli su sa ido kan duk wata dabbar da za a yanka a mahauta.
- Za a kama masu gidan abinci da masu sayar da abinci tare da kai su kotu idan suka sayar da naman dabbar da aka yanka ba tare da sa idon malaman lafiya da jami’an muhalli ba.
- Dole ne a bayar da rahoto ga likitocin dabbobi ko jami’an muhalli idan wata dabba ta mutu domin gudanar da bincike; haka kuma an gargadi al’umma kan cin naman matacciyar dabba.
Haka kuma ma’aikatar abinci da aikin gona ta Ghana ta sanar da cewa za ta kara daukar matakai daga bangarenta domin kiyaye sake bullar wannan cuta.
Wadannan matakan sun hada da:
- Yin rigakafin anthrax ga dabbobi.
- Kara kaimi wurin bincike da sa ido kan dabbobi da mutane kan cutar anthrax.
- Wayar da kan jama’a kan hanyoyin da da za a bi domin kare kai daga cutar ta anthrax.
Mece ce cutar Anthrax?
Anthrax cuta ce mai yaduwa wadda wata kwayar cutar bakteriya mai suna Bacillus anthracis ke haifarwa.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cuta ce wadda ake yada ta daga dabbobi zuwa mutane kuma ta fi kama dabbobi da suka hada da shanu da tumaki da awaki.
Alamomin cutar a bil adama sun hada da ciwon kai da ciwon jiki da zazzabi da matsalar numfashi da jiri da mura.
Ana iya kiyaye kamuwa da cutar ta hanyar yi wa dabbobi da bil adama rigakafin cutar.