Wani babban masanin kimiyya a hukumar lafiya ta Duniya WHO ya ce zazzabin Dengue zai zama babbar barazana a kudancin Amurka da kudancin Turai da kuma wasu sassan yankunan Afirka a shekaru masu zuwa.
Masanin ya yi la'akari da yadda yanayin lokutan zafi ke bai wa sauron da ke dauke da cutar damar yada ta ga dan'adam.
Cutar ta dade da zama annoba a yawancin kasashe yankunan Asiya da Latin Amurka, wanda ke haddasa mutuwar mutane kusan 20,000 a kowace shekara
Adadin cutar ya karu kusan sau takwas a duniya tun daga shekarar 2000, sakamakon sauyin yanayi da karuwar yawan jama'a da kuma birane.
A shekarun baya ba a cika daukar bayanai kan cutar ba, sai dai a shekarar 2022, an fitar da rahoton da nuni kan cewa mutum miliyan 4.2 ne a duniya suka kamu da cutar, jami'an kiwon lafiya dai sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake samun makamancin adadin a wannan shekara.
Karin matsa lamba
A yanzu haka Bangladesh na fama da mafi munin barkewar cutar, inda ya kashe mutane sama da 1,000. kazalika an samu rahoton barkewar cutar a Sudan.
"Muna bukatar a fito a yi magana sosai game da wannan cuta ta dengue," in ji Jeremy Farrar, ƙwararre kan cututtuka masu yaduwa wanda ya soma aiki da WHO a watan Mayun shekarar nan, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
"Muna bukatar fargar da kasashe kan yadda za su tunkari wasu karin matsin lamba da za su biyo baya… a nan gaba a manyan biranen da dama."
A baya , Farrar ya kwashe tsawon shekaru 18 yana aiki a Vietnam kan cututtuka da ake samu a wurare masu zafi ciki har da cutar zazzabin dengue.
Daga baya ya jagoranci kungiyar ba da agaji ta lafiya ta duniya 'Wellcome Trust' sannan yana daga cikin masu bai wa gwamnatin Birtaniya shawara kan matakan kariya na COVID-19 kafin ya shiga WHO a watan Mayun wannan shekara.
Muhimmacin samun kulawa
Farrar ya ce akwai yiwuwa cutar ta iya “bazuwa” kuma ta zama annoba a sassan Amurka da Turai da kuma Afirka - dukkan kasashen da aka samu bullar cutar a yankunansu - dumamar yanayi na kara samar da sabbin wuraren ga sauron da ke dauke da cutar su dada yaduwa.
A cewar masanin yakan zai kara wa tsarin asibitoci a kasashe da yawa matsin lamba.
"Samun kulawar asibiti yana da matukar muhimmaci, ana butatar adadi ma'aikatan jinya masu yawa da za su kula da marasa lafiya," in ji shi. "Zai yi matukar damuwa idan hakan ya zama babban batu a yankin kudu da hamadar Saharar Afirka."
Yawancin mutanen da suka kamu da zazzabin dengue ba sa nuna wata alama ta cutar, hakan na nufin adadin mutanen da suka kamu da cutar ya zarce wadanda aka rahotanni suka bayyana.
Mutanen da suka yi fama da zazzabi da tsanani ciwon jiki da gabobi ana kiransa da "zazzabin kabobi." A lokuta mafi tsanani - kasa da kashi 1 cikin 100 % - ke iya kisa.
Kashe kudi bisa tsari
Babu wani takamaiman maganin warkar da cutar dengue, sai dai akwai rigakafi.
A farkon makon nan, WHO ta ba da shawarar amfani da allurar rigakafin Qdenga na kamfanin hada magunguna na Takeda ga yara ƴan shekara 6 zuwa 16 a yankunan da cutar ke zama babbar baraza ga lafiyar al'umma.
Kazalika masu sa ido daga kungiyar kasashen turai EU sun amince da allurar, sai dai a shekarar nan ne kamfanin Takeda ya janye aikace-aikacensa a Amurka kan batun tattara bayanai.
Takeda ya ce har yanzu yana tattaunawa da Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka game da rigakafin.
Farkar da wasu sabbin yankuna a duniya kan hanyoyin takaita yaduwar sauro da kuma magance cutar Dengue, na nufin amfani da duk wani kudi da aka ware don kula da kiwon lafiyar jama'a ta hanyar da ta dace, in ji Farrar.
Nau'in sauron Aedes aegypti ke yada cutar zazzabin Dengue wanda ya bambanta da sauron da ke haddasa cutar zazzabin cizon sauro.
Misali, sauron na cizon mutane a cikin gida, kuma a kowanne lokaci ba wai cikin dare kawai ba, sannan sauron na rayuwa a kan ruwa mara zurfi.
Farrar ya ce muhimman hanyoyin da za a bi wajen ba da kariya daga cutar sune fitar da muhimmaci kan tsare-tsare a asibibtoci da sabbin kirkiren kimiyya da dai sauransu kamar tsara birane da kuma toshe duk wata kafa da ruwa zai iya tsayawa a ciki ko a wajen gida.
"Muna bukatar hada ma'aikatu daban-daban wadanda basu saba yin aiki tare ba don cimma hakan," in ji shi.