Shugaban Hezbollah na Labanon ya ce abin da ya faru a Labanon a ranar Talata da Laraba za a iya daukar sa a matsayin "ayyana yaki". / Hoto: Reuters

Alhamis, 19 ga Satumban 2024

1434 GMT — Shugaban Hezbollah na Labanon ya ce abin da ya faru a Labanon a ranar Talata da Laraba za a iya daukar sa a matsayin "ayyana yaki".

"Da wannan farmakin, makiya sun ketare dukkan... jan layi," in ji Hassan Nasrallah a fitowarsa ta farko a talabijin bayan kai hare-haren, yana zargin hakan da kokarin "kashe mutane a kalla 5,000" a cikin "babbar takalar ƙungiyar da ba a taɓa ganin irin ta ba.

1319 GMT - Isra'ila ta ba da rahoton sake harba makaman roka daga Lebanon

An harba makaman roka guda 10 daga Lebanon inda suka sauka a yankunan da ke Upper Galilee da ke arewacin Isra'ila, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka bayyana.

Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta ce an lalata "gine-gine" a cikin "yankunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna na Zar'it" sakamakon fadowar rokoki daga Lebanon. Ba a samu rahoton jikkata ba.

1127 GMT — Yawan wandanda suka mutu a fashewar na'ura a Lebanon ya karu zuwa 37

Ministan lafiya na Labanon Firass Abiad ya ce mutum 37 ne suka mutu sannan wasu fiye da 3,500 suka samu raunuka a wani sabon adadin da aka samu, bayan da aka tayar da na'urorin sadarwa na ‘yan kungiyar Hizbullah a fadin kasar ta Lebanon, a hare-haren da ake zargin Isra’ila ke da hannu.

Abiad ya ce an kashe mutum 25 a ranar Laraba da kuma 12 a ranar Talata, wanda ya bayyana adadin wadanda suka mutu gaba daya ya kai 32.

1241 GMT 1241 GMT - Ministan Harkokin Wajen Italiya don tattauna sabbin tsare-tsare kan Gaza tare da Ƙasashen Yamma

Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya bayyana cewa, zai tattauna yiwuwar samar da sabbin tsare-tsare na zaman lafiya a Zirin Gaza da wasu kasashen Yammacin Duniya biyar da aka fi sani da kungiyar Quint.

Quint ƙungiyar yanke shawara ce ta yau da kullum wacce ta ƙunshi Amurka, Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya. "Muna cikin damuwa game da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

"A daren yau, zan kasance a birnin Paris don tantance halin da ake ciki. Kasashe biyar za su gana kuma mu ga ko za a iya daukar sabbin tsare-tsare,” Tajani ya fada wa manema labarai a Rome.

"Muna ci gaba da aiki tare don samar da zaman lafiya, tsagaita bude wuta, da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji shi.

TRT Afrika da abokan hulda