Mutane sun yi ta ɗaukar gawarwakin wadnda suka mutun daga asibitin Ah Ahli zuwa asibitin Al-Shifa hospital ranar 17 ga watan Oktoban 2023. / Photo: AFP

Isra'ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 500 a wani harin sama da ta kai a asibitin Al Ahli a Gaza, inda majinyata da mutanen da suka ji raunuka da ma waɗanda ke samun mafaka sakamakon hare-haren Isra'ila duk ke ciki a lokacin, lamarin da ya jawo Allah wadai da tir a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.

Ga dai manyan martanin da wasu ƙasashe suka yi:

Falasɗinu

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya ce kai wa asibiti hari "mummunan kisan ƙare dangi ne na yaƙi" wanda ba za a lamunta ba, yana mai cewa babu wata tattaunawa da za a amince da ita in dai ba ta dakatar da yaƙin ba ce.

"Isra'ila ta ƙetare duk wasu iyakoki. ... Ba za mu fice daga nan ko mu yarda wani ya kore mu ba," ya ƙara da cewa.

Firaiministan Falasɗinu Mohammad Shtayyeh ya kira harin da Isra'ila ta kai wani asibitin Gaza a matsayin "mummunan laifin yaƙi abin tsoro, kuma kisan ƙare-dangi," yana mai cewa alhakin ya kuma rataya a kan ƙasashen da ke goyon bayan Isra'ila irin su Amurka ma.

Turkiyya

“Kai hari kan asibitin da mata da yara da sauran fararen-hular da ba su ji ba ba su gani ba ke ciki shi ne mafi kololuwar cin zali da take darajar dan'adam na hare-haren Isra'ila,” in ji Erdogan a shafinsa na X a ranar Talata.

Erdogan ya yi kira da dukkan mutanen duniya da su ɗauki matakin dakatar da “munanan hare-haren da ba a taɓa ganin irinsu ba” da Isra’ila ke kai wa Gaza.

"Mun damu da mutuwar ɗaruruwan Falasɗinawa da kuma ɗaruruwan da suka jikkata sakamakon harin da aka kai asibiti yau a Gaza, sannan mun yi Allah wadai da dukkan munanan hare-haren da ake kai wa da kakkasaur murya," in ji sanarwar Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

“Ya zama wajibi a gurfanar da duk wanda ke da hannu a kai wa fararen-hula da asibitoci da makarantu hare-hare a gaban kotun ƙasa da ƙasa kan nuna rashin tausayi da jinƙai,” ta ƙara da cewa.

Pakistan

"Kai hari asibiti inda fararen-hula ke samun mafaka da kuma kula da marasa lafiya rashin tausayi ne kuma abu ne mara dalili," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan a wata sanarwa.

Ta ƙara da cewa "Kai hari kan wajen da fararen hula suke da cibiyoyin lafiya mummunan take hakkin dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa ne."

Labari mai alaka: Yadda aka mamaye Falasdinawa

"Muna kira ga dukkan al'ummar duniya da su ɗauki matakan gaggawa na kawo ƙarshen hare-hare da ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa Gaza da irin cin zalin da hukumominta ke yi a Gaza a ƴan kwanakin nan," a cewar ma'aikatar.

Tsohon Ministan Harkokin Wajen kuma shugaban jam'iyyar masu sassauvcin ra'ayi ta Pakistan People's Party, Bilawal Bhutto Zardari, shi ma ya yi tur da harin da aka kai asibitin, yana mai kiransa da "babbar shaida ce ta irin muguntar da Isra'ila ke yi."

Saudiyya

Saudiyya ta yi Allah wadai da kakkausar murya da "mummunan laifi" na harin da dakarun Isra'ila suka kai Asibitin Al Ahly a Gaza da ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta fitar a wata sanarwa.

"Wannan mummunan lamarin ya tilasta wa ƙasashen duniya dole su bar munafuncin da suke yi da nuna son kai wajen fayyace dokokin hakkin ɗan'adam na duniya idan aka zo batun munanan ayyukan da Isra'ila ke aikatawa," in ji sanarwar.

Kuwait

Kuwait ma ta bi sahu wajen yin tur da wannan mummunan hari da dakarun Isra'ila suka kai.

"Kai hari kan asibitoci ko wuraren taruwar jama'a da dakarun ƴan mamaya ke yi take dokokin duniya ne jinƙai ne," in ji sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen ta fitar.

Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai

Shugaban Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai OIC, Hissein Taha, ya kira harin da "laifin yaƙi" da kuma "take haƙƙin ɗan'adam."

Taha ya ɗora laifin a kan mamayar Isra'ila, inda ya ce tana aikata munanan hare-hare a kan Falasɗinawa, lamarin da ya ci karo da mutunta ɗan'adam da dokokin duniya na jinƙai, a sanarwar da ya fitar.

Masar

Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi ya ce Alkahira na sa ido sosai kan abin da ke faruwa cikin tsananin alhini.

"Don haka na yi Allah wadai da kakkausar murya a kan wannan hari, wanda ƙarara take dokokin duniya ne, kuma ina neman a bi tsarin dokokin mutunta ɗan'adam na duniya," in ji Sisi a shafinsa na X.

Shugaban na Masar ya jaddada matsayar ƙasarsa da ta al'ummarsa a kan batun, tare da neman a yi gaggawar dakatar da hare-haren Isra'ila a Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Qatar

Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ta yi Allah wadai da mummunan harin bam da Isra'ila ta kai Asibitin Al Ahli Baptist a Gazar da aka yi wa ƙawanya.

"A kan wannan lamarin, ma'aikatar na kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki nauyin d ake kansu su hana Isra'ila sake aikata wasu laifukan a kan fararen hula," ma'aikatar ta faɗa a wata sanarwa.

Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta yi kira da "a nuna fushi na rana ɗaya a kan maƙiya."

"Gobe Laraba za ta zama ranar nuna fushi a kan maƙiya," Hezbollah ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar.

UAE

Ita ma ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE Allah wadai ta yi da kakkausar murya a kan harin na Isra'ila, tana cewa tana "bayyana kaɗuwa da alhini a kan rayukan da aka rasa tare da miƙa saƙon ta'aziyyarta da jaje ga iyalai da waɗanda abin ya shafa, da kuma fatan waɗanda suka jikkata su samu sauƙi cikin gaggawa."

Ta yi kira "kan yin gaggawar tsagaita wuta da tabbatar da cewa ba a kai hari kan fararen hula da wuraren taruwarsu.

Jordan

Sarkin Jordan Sarki Abdullah II shi ma ya yi Allah wadai da harin na Isra'ila kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba da marasa lafiyan da ake kula da su a asibiti.

"Mai martaba ya ce wannan mummunan hari ne da ba za a lamunta ba, kuma dole Isra'ila ta dakatar da mugunta da cin zalin da take yi a Gaza, wanda ya yi hannun riga da dokokin darajta ɗa'adam da na jinƙai na duniya," kamar yadda aka wallafa a shafin intanet na sarkin.

Ya yi gargaɗin cewa yaƙin ya shiga wani mataki mai muni da zai sa yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya ya shiga rikici, yana maa cewa dole ƙasashen duniya su kawo ƙarshen wannan zubar da jinin.

Iran

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da ta ce ya kashe ɗaruruwan mutane da jikkata wasu ɗaruruwan, wadanda fararen hula ne da ba su ji ba, ba su gani ba,kamar yadda kafar yaɗa labaran Iran ta rawaito.

"Wutar hare-haren bam na Amurka da Isra'ila da ta sauka da daddaren nan a kan Falasɗinawan da babu ruwansu waɗanda ake jinyarsu a asibiti a Gaza, tabbas ita za ta lashe dukkan masu aƙidar kafa ƙasar Isra'ila.

"Ba za a yarda da yin shirun duk wani ɗan'adam mai cikakken ƴanci ba a wannan lokaci da ake aikata munanan ayyukan yaƙi. Iran, a matsayinta ta ƙasar Musulmai, tana cikin baƙin ciki," in ji sanarwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi.

Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya ɗage ziyarar da ya yi niyyar kai wa Jordan saboda harin da aka kai asibitin Gaza, yana mai miƙa ta'aziyyarsa kan waɗanda suka mutu a wata sanarwa da Fadar White House ta kira "fashewar wani abu a asibiti".

"Shugaban ƙasa na nuna alhini da jimami kan mutanen da suka mutu a wata fashewa a asibitin Gaza, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi," in ji sanarwar.

Birtaniya

Dan siyasar Birtaniya Keir Starmer a shafinsa na X ya ce abin da ya faru a Gaza yana da "muni" kuma ba za a iya goyon bayan hakan ba.

"Dole a bi dokokin ƙasa da ƙasa. Dole a kare asibitoci da rayukan fararen hula," in ji Starmer.

Canada

Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce harin da Isra'ila ta kai asibiti a Gaza "abin tsoro ne kuma ba za a yarda da shi ba."

Trudeau ya shaida wa manema labarai cewa "ba za a yarda da akai hari asibiti ba."

Shugaban hukumar kare hakkin ɗan'adam ta MDD

"Kalmomin bakina sun ƙare. Da daddaren nan an kashe ɗaruruwan mutane - abin ban tsoro - a wani hari da aka kai Asibitin Al Ahli a Birnin Gaza, a ciki akwai marasa lafiya da jami'an kula da lafiya da iyalai wadanda ke samun mafaka a asibitin. Wadanda su ne suka sake zama abin tausayi a lamarin. Wannan abu ne da ba za a yarda da shi ba sam," a cewar shugaban hukumar kare hakkin ɗan'adam ta MMajalisar Dinkin Duniya Volker Turk.

Jamus

Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus ta ce ta kaɗu matuƙa da rahotannin cewa ɗaruruwan mutane sun mutu a Asibitin Al Ahli da ke Gaza.

"Bai kamata ko ma waye ya kai hari wajen da fararen hula musamman asibiti da ke cike da marasa lafiya da jami'an kula da lafiya suke ba, a kowane irin yanayi kuwa, ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X.

"Dole a kare fararen huka a lokacin yaƙi," ta ƙara da cewa.

WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ita ma ta yi Allah wadai da mummunan harin tare da neman a gaggauta bai wa fararen hula da cibiyoyin lafiya kariya a yankin gAzan da aka yi wa ƙawanya.

"WHO ta yi Allah wadai da kakkausar murya a kan harin da aka kai Asibitin Al Ahli," kamar yadda hukumar ta MDD ta fada a wata sanarwa.

"Asibitin yana aiki kuma cike yake da marasa lafiya da ma'aikatan lafiya da masu neman mafaka. Rahotannin farko-farko sun nuna cewa ɗaruruwan mutane sun mutu wasu kuma sun jikkata.

Tarayyar Afirka

Shugaban Ƙunfiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya zargi Isra'ila da aikata "laifin yaƙi."

Babu wata kalma da za ta bayyana Allah wadai dinmu cikakke kan harin da Isra’ila ta kai a asibitin Gaza a yau, inda ta kashe daruruwan mutane. Kai hari a asibiti, wanda ake gani a matsayin tudun-mun-tsira a Dokokin Duniya, aikata laifin yaki ne. Dole kasashen duniya su dauki mataki a yanzu, Faki ya bayyana a shafinsa na X.

Scotland

A shirye Scotland take ta taimaka da kariya da mafaka ga ƴan gudun hijirar Gaza, in ji Babban Ministan ƙasar Humza Yousaf.

"Babu wani dalili na kai wannan harin. Babu shi sam. Idan har mutane ba su tsira ba a asibiti ko a ina za su samu tsira? Dole ne a fito ɓaro-ɓaro a yi Allah wadai da harin nan ta kowane hali," ya faɗa a shafinsa na X.

"A baya, mutane a Scotland da fadin Birtaniya mun buɗe zuciyoyinmu da gidajenmu. Mun yi wa ƴan Syria maraba, da ƴan Ukraine da ma ƴan wasu ƙasashen da dama... Dole mu sake yin hakan," ya ƙara da cewa.

"Yanzu haka akwai mutum miliyan ɗaya da suka rasa wajen zama a Gaza. Don haka, ina kira a yau ga ƙasashen duniya da su yi aiki da shirin taimakon ƴan gudun hijira na fadin duniya saboda ƴan Gaza," ya ce.

TRT World