Shugaban Chile ya kira firaministan Isra’ila mai aikata laifukan yaƙi

Shugaban Chile ya kira firaministan Isra’ila mai aikata laifukan yaƙi

Abin da Benjamin Netanyahu ke yi laifin yaƙi ne, laifi ne ga ɗan’adam, a cewar Shugaba Gabriel Boric.
Shugaban Chile Gabriel Boric yana daga sugabannin duniya da suke caccakar firaministan Isra’ila. / Hoto: AA

Shugaban Chile Gabriel Boric ya bayyana Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu mai aikata laifukan yaƙi saboda abin da yake yi a Gaza da sauran yankunan Falasɗinu.

Da yake magana a wajen taron “Kirsimetin Falasɗinu: Hasken Kyakkyawan Fata daga Bethlehem zuwa Chile" a ranar Laraba, Boric ya soki Netanyahu kan hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda a yanzu suka shiga wata na 14 a jere.

“Babu wata dama ta ɗaukar matakai rabi-da-rabi a wajen kare ɗan’adam, kamar yadda ya faɗa a Filin Wasa na Falasɗinu a babban birnin ƙasar Santiago.

Boric ya kuma yi kira a ruɓanya ƙoƙari don samun zaman lafiya.

“Muna matuƙar jin raɗaɗi kuma mun kaɗu ba kawai da abin da yake faruwa a Gaza ba, har ma da abubuwan da suke faruwa a Gaɓar Yamma,” a cewarsa, yana bayani kan haramtattun ‘yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yamma da Kgin Jordan da aka mamaye da kuma yadda sojojin Isra’ila ke kai wa Falasɗinawa hari a can.

Boric ya jaddada cewa abin da Netanyahu yake yi laifukan yaƙi ne kuma “dabbanci” ne, yana mai ƙarawa da cewa: “Na zaɓi mutunta ɗan’adam. Abin da Netanyahu ya yi laifin yaƙi ne, laifi ne ga ɗan’adam.”

Tun Oktoban 2023, hare-haren Isra’ila a Gaza sun kashe fiye da mutum 45,000 sun kuma jafa mafi yawancin yankin cikin mummunar tagayyara, inda mutanen da suka tsira suke fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwa.

Tun 2021, Falasɗinawa da ke zaune a Chile suke gudanar a taron “Hasken Kyakkyawan fata”.

Kimanin Falasɗinawa dubu ɗiyar biyar ne suke zaune a ƙasar.

TRT Afrika