A kokarinta na karfafa tasirinta a Gabashin Birnin Kudus da ta mamaye, gwamnatin Isra'ila ta gabatar da wani shiri na kasafin kudi wanda zai "sauya fuskar birnin Kudus" cikin shekara biyar masu zuwa.
A cewar wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Lahadi, an ware kasafin shekel biliyan 3.2 na Isra'ila, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 843, don saka hannun jari a yankin Gabashin Kudus da ta mamaye, tsakanin shekarar 2024 zuwa 2028.
Sanarwar ta ce makasudin wannan shirin shi ne don a magance rashin daidaito tsakanin al'umma da kuma bunkasa tattalin arziki a Gabashin Kudus da aka mamaye.
Kan batun shirin, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, "Shawarar za ta sauya fasalin Birnin Kudus."
Netanyahu ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen kara adadin mutanen da suka samu takardar shaidar kammala karatun gaba da sakandare.
Falasdinawa da ke zaune a yankin Gabashin Kudus na kokawa da yunkurin da Isra'ila ke yi na sauya jadawalin makaratu, duk da kokarin kiyaye su da take yi.
Sanarwar Isra'ila na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata kungiyar da ke sa ido kan yankunan Isra'ila ta bayyana cewa gwamnatin Benjamin Netanyahu na bayar da tallafin mallakar filayen da ke gabar Yammacin Kogin Jordan ta hanyar ware karin kasafin kudi na dala miliyan 190.
Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin Isra'ila ta shirya wani shiri na zuba jari na kusan shekel miliyan 700 da ba a taba ganin irinsa ba a matsugunan Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
“Bisa ga daftarin da muka samu, shirin ya kai shekel din isra’ira miliyan 671.63 (kimanin dalar Amurka miliyan 190) daga kasafin kudin shekarar 2023-2024, amma akwai wasu sharuddan da har yanzu ba a tantance adadin kudaden da za a raba ba, don haka ana sa ran jimillar kudaden za su wuce yadda ake tsammani, "a cewar kungiyar.
Jumullar kudin shekel miliyan 92, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 24 ne aka ware a matsayin kudin tallafi da ba a tanttace,hakan na nufin za a iya amfani da kudaden don aiwatar da kowace irin manufa, in ji kungiyar.
Kungiyar ta soki matakin, tana mai cewa: "Maimakon saka hannun jari a makomar Isra'ila, gwamnatin kasar tana zuba kudade a yankunan da ke ci gaba da ikon mamayarta, tare da rura wutar rikici da kara kai hare-hare kan Falasdinawa."
Alkaluma sun yi nuni kan cewa kimanin 'yan Isra'ila 700,000 ne ke zaune a matsugunai 164 da kuma sansani 116 a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.
A karkashin dokokin kasa da kasa, ana kallon duk wani wuri ko matsuguni da Yahudawa suka mamaye a yankin gabar kogin a matsayin haramtacce wuri.