Shekara 42 da suka wuce, ma'aikaciyar jinya ta dauki jaririn Maria Angelica Gonzalez daga hannunta bayan da ta haihu. / Hoto AP

"Sannu, Mama.”

Abin da ya yi kama da gaisuwa tsakanin uwa da danta, amma sai ya zama wani abin ban al'ajabi.

Shekara 42 da suka wuce, ma'aikatan asibiti sun karbe jaririn Maria Angelica Gonzalez daga hannunta, bayan ta haihu. Kuma daga bisani suka ce mata ya rasu. Amma yanzu, ta gana da shi a gidanta a birnin Valdivia a kasar Chile.

"Ina kaunarki sosai," Jimmy Lippert Thyden ya shaida wa mahaifiyarsa a cikin harshen Spaniya yayin da suke rungume da juna suna kuka.

"Abin ya kada ni sosai…abin ya ba ni mamaki sosai," kamar yadda Thyden ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na The Associated Press a waya ta bidiyo. "Yaya za ka rungumi mutum ta hanyar da za ka ji kamar ka rungume shi duk tsawon shekara 42?"

Ya fara neman danginsa ne a watan Afrilu bayan ya karanta labaran dangane da jariran Chile da aka raba da iyayensu kuma aka sada su da danginsu da taimakon kungiyar Nos Buscamos.

Kungiyar ta gano cewa an haifi Thyden a matsayin bakwaini ne a wani asibiti a birnin Santiago, babban birnin kasar Chile kuma daga nan sai aka saka shi a cikin kwalba.

Asibitin ya bukaci mahaifiyarsa ta bar asibitin bayan da ta koma don ta karbi jaririnta, sai aka ce mata danta ya mutu, kuma an jefar da gawarsa, kamar yadda wasu bayanai da Thyden ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AF suka tabbatar.

"A takardar izinin daukata an ce ba ni da wani dangi da ke raye. Kuma na gano cewa a watannin da suka wuce ina da mahaifiya da kuma 'yan uwana maza hudu da mace daya," in ji Thyden a wata ganawa da ya yi a birnin Ashburn a jihar Virginia, inda yake aiki a matsayin lauya wanda ke kare mutanen da ba su da karfin daukar lauya.

Ya ce na ga hakan ne "an takardun daukarsa na jabu ne".

Kungiyar Nos Buscamos ta yi kiyasin an dauke dubban jarirai daga iyayensu a Chile a shekarun 1970 da 1980, kamar yadda wani binciken 'yan sanda a Chile ya bayyana wanda ya yi nazari kan hoton fasfo din yara 'yan Chile da suka bar kasar kuma ba su dawo ba.

"Ainiyin labarin shi ne an sace yaran ne daga iyayensu matalauta, ba da sanin iyayensu mata matalauta ba. Ba su san yadda za su kare kansu ba," in ji Constanza del Rio darakta kuma wanda ya kafa kungiyar Nos Buscamos.

Safarar yaran ya yi arashi da sauran nau'ukan take hakkin dan Adam wadanda suka faru zamanin mulkin Janar Augusto Pinochet na shekara 17, wanda a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 1973, ya jagoranci kifar da gwamnatin Shugaba Salvador Allende.

Lokacin mulkin kama karyan da ya yi, an kashe akalla mutum 3,095, kamar yadda gwamnati ta bayyana kuma an azabtar da wasu yayin da aka tsare wasu saboda dalilan siyasa.

A shekara tara da suka wuce, kungiyar Nos Buscamos ta jagoranci sada yara da danginsu na asali guda 450, in ji del Rio.

Wasu kungiyar su ma suna irin wannan aiki, ciki har da kungiyar Hijos y Madres del Silencio a Chile da Connecting Roots a Amurka.

Kungiyar Nos Buscamos tana aiki tare da wani shafi mai taimaka wa wajen gano asali mutum mai suna MyHeritage, wanda take samar da kayan gwajin kwayoyin halitta na DNA kyauta a gida ga yaran da aka raba da iyayensu da kuma wadanda ake zargi an yi safararsu a Chile.

Gwajin kwayoyin DNA da aka yi wa Thyden ya tabbatar da cewa shi dan Chile ne kuma gwajin ya yi daidai da wani dan uwansa wanda shi ma yake amfani da shafin MyHeritage.

Thyden ya aika wa dan uwansa takardar izinin daukarsa wadda take dauke da adireshin mahaifiyar da ta haife shi da kuma wani sunan da yake da yawa a Chile wato sunan: Maria Angelica Gonzalez.

Ashe dan uwan nasa yana da mai suna Maria Angelica Gonzalez a danginsa na uwa kuma ya taimaka masa wajen haduwa da ita.

Amma Gonzalez ba ta daukar wayarsa har sai bayan da ya tura mata hoton matarsa da 'ya'yansa mata.

"Daga nan ne sai komai ya warware," in ji Thyden, wanda ya tura mata karin hotunan mutanen da suka rike shi, da aikinsa a rundunar sojin ruwan Amurka da na aurensa da sauran abubuwa masu sosa rai da suka faru a rayuwarsa.

"Na yi kokarin ba ta labarin abubuwan da suka faru tsawon shekara 42 da aka raba mu," in ji shi.

Ya yi tafiya zuwa Chile tare da matarsa, Johannah da 'ya'yansa mata biyu, Ebba Joy, mai shekara 8 da kuma Betty Grace, mai shekara biyar, don su gana da sabbin danginsu da aka gano.

Yayin da ya taka kafarsa a gidan mahaifiyarsa, an tarbi Thyden da wasu balan-balan guda 42 masu launi mai ban sha'awa, kowace daya tana ishara kan tsawon lokacin da aka raba shi da danginsa a Chile.

"Samar da balan-balan din yana da karfafa gwiwa musamman saboda yadda ka kasance da danginka saboda tattauna duka lokacin da kuka kasance ba kwa tare," in ji shi.

Thyden ya tuna abin da mahaifiyarsa ta yi lokacin da ta ji muryarsa: "Dana ba ka da masaniya kan yadda nake kuka a kanka. Na kan tashi cikin dare a lokuta da dama ina addu'o'in Ubangiji ya ba ni tsawon rai don na gano abin da ya faru da dana."

Gonzalez ta ki yarda a tattauna da ita kan wannan labari. Thyden, tare da matarsa da 'ya'yansa mata sun kai ziyara gidan zoo na Santiago inda danginsa na Amurka suka dauke.

Wannan karon kawansa ta jini ce ta yi musu jagora. Yayin da suka koma gidan Gonzalez, Thyden ya fahimci cewa shi da mahaifiyarsa suna kaunar yin girki.

"Hannuna da na mahaifiyata suna cikin tukunya daya muna hada kayan abinci," in ji shi yayin da suke girkin. Ya dauki alkawarin yin irin abincin danginsu don kara kulla alaka da gidansu da kuma al'adarsa.

Thyden ya ce iyayen da suka dauke shi sun taimaka masa wajen gano danginsa wadanda suka shiga "wani hali" sanadin haramtaccen tsarin daukar yara. "Iyayena suna son 'ya'ya amma ba su bi wannan hanyar ba," in ji shi.

"Ba su cutar da wani ba, ko kuma yi wa wani kwace ba." Iyayen da suka dauke shi sun ki yin magana ta bakin mai magana da yawunsu.

Yayin da Thyden ya yi nasarar gano danginsa na asali, ya fahimci cewa ba lalle ne hakan ya tafi daidai da wasu da suke cikin irin halinsa ba. "Da abin ya kasance mummunan labari," in ji shi.

"Akwai mutanen da suke gano abubuwa marasa dadi game sa asalinsu." Yayin da Thyden da del Rio suka hadu a Chile tare da wasu masu bincike su bakwai wadanda suke kokarin neman mafita ga dubban yaran da aka dauka da takardun bogi kamar shi.

"Ba ma bukatar kudi, muna so ne mu tabbatar da asalin mutane kuma yadda wannan abu ba zai ci gaba da faruwa a Chile ba a nan gaba," in ji del Rio.

"Muna kokarin gyara al'amarin. Ba kaiwai a kan Jimmy da danginsa ba, amma muna so ne mu canja al'amura a wannan kasa."

Har ila yau Thyden ya gana da Juan Gabriel Valdes wato jakadan Chile a Amurka don ya yi magana kan yawaitar matsalar raba yara da danginsu.

Ya ce babu wani tsari ko na kudi ko makamancinsa na taimaka wa yaran da aka dauko daga Chile na kai ziyara gida. Ya ce sai da ya sayar da wata babbar mota kafin ya biya kudin jirgin iyalinsa da sauran dawainiyarsu.

"Ya kamata mutane su rika yanke shawara…yaya sunansu zai kasance, wacce kasa ce za ta kasance kasarsu. Ya dace su samu dama biyu ne dangane da kasashen," in ji shi.

"Ya kamata su samu duka damarmakin da 'yan Chile suke samu saboda abin da ya same su, wanda ba zabin kansu ba ne."

Ofishin jakadancin Chile a Washington bai ce komai ba yayin da muka nemi yin magana da su.

TRT World