Shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter ya mutu, kamar yadda jaridar Atlanta Journal-Constitution ta ba da rahoto.
Ya mutu yana da shekara 100.
Marigayin, ɗan jam'iyyar Democrat, ya yi shugabanci daga Janairun 1977 zuwa Janairun 1981 bayan ya kayar da shugaba mai ci ɗan jam'iyyar Republican Gerald Ford a zaɓen 1976.
An fitar da Carter daga ofis bayan shekara huɗu a wani zaɓe da gagarumar nasara, yayin da masu zaɓe suka rungumi wanda ya yi takara da shi a jam'iyyar Republican Ronald Regan, wanda tsohon tauraron finafinai ne kuma tsohon gwamnan California.
Jimmy Carter shi ne shugaban Amurka da ya fi tsawon rai bayan barin ofis.
A lokacin shugabancinsa na wa'adi ɗaya ne aka cim ma gagarumar yarjejeniyar Camp David tsakanin Isra'ila da Masar a 1978.
Amma an fuskanci matsalolin koma-bayan tattalin arziki da rashin farin jininsa da kuma abin kunyar da ya faru na garkuwa da Amurkawa da Iran ta yi, wanda ya mamaye kwanaki 444 na ƙarshen wa’adinsa a ofis.
A 'yan shekarun nan, Carter ya fuskanci matsalolin lafiya da yawa ciki har da sankarar fata nau’in melanoma, wacce ta yaɗu zuwa hantarsa da ƙwaƙwalwarsa.
Carter ya yanke shawarar yin jinya a gida a cikin Fabrairu 2023 maimakon yin jinya a asibiti.
Carter ya shefe shekaru da dama yana ayyukan jinƙai.
An ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2002 saboda "ƙoƙarin da yake yi na samar da hanyoyin warware rikice-rikice a duniya, don ciyar da dimokuraɗiyya da 'yancin ɗan’adam gaba, da kuma bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa."