Jumullar mutum 179 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da mutum biyu kacal - ɗaya fasinja ɗaya kuma ma'aikacin jirgi - aka ceto su, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta sanar, bayan da wani jirgin saman Jeju Air ya yi hatsari a lokacin da yake sauka inda yake dauke da mutum 181.
"A cikin mutane 179 da suka mutu, an gane fuskokin 65," in ji hukumar kashe gobarar.
irgin saman Jeju Air ɗauke da fasinjoji 181 da suka hada da ma'aikata shida, ya kama da wuta a lokacin da yake sauka bayan da aka ruwaito cewa ya fuskanci matsalar na'urar da ke taimaka wa jirgi sauka da misalin karfe 9:07 na safe agogon kasar a gundumar Muan - mai tazarar kilomita 288 kudu maso yammacin Seoul babban birnin Koriya ta Kudu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Yonhap.
Jirgin wanda ya taso daga Bangkok ya rinƙa jan ciki a kan titinsa inda ya daki bango sai ya kama da wuta.
A bidiyon da kafafen watsa labaran ƙasar suka nuna an ga jirgin yana tafiya da jan ciki a kan titinsa inda ya kama da wuta
Yawancin fasinjojin 'yan Koriya ne baya ga wasu 'yan kasar Thailand biyu.