Akalla mutum 30 sun rasu, 50 kuma suka samu raunuka bayan hatsarin da wani jirgin kasa ya yi dauke da fasinjoji a kudancin lardin Sindh na Pakistan.
Akalla taragai 10 na jirgin fasinja mai suna Hazara Express suka sauka daga layin dogo a lokacin da jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa Rawalpindi bayan ya taso daga birnin Karachi.
Ministan sufurin jiragen kasa Khawaja Saad Rafiq ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu inda ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon wata matsala ta jirgin ko kuma abin da ya kira “kafar-ungulu”.
Kafar watsa labarai ta kasar ta ruwaito ma’aikatan lafiya suna cewa daga cikin wadanda suka mutu da kuma samun raunuka akwai mata da yara kuma an kai su asibitin birnin Nawabshah mai nisan kilomita 15 daga wurin da hatsarin ya faru.
Hukumomi sun yi fargabar za a iya samun karuwa a adadin wadanda suka rasu sakamakon akwai gomman fasinjoji wadanda suka makale a cikin taragan da suka fadi.
Masu aikin ceto na fuskantar matsaloli wurin ceto wadanda suka jikkata da kuma kai su asibiti saboda wurin da lamarin ya faru ya yi nisa da gari sosai.
An sha samun hatsarin jirgin kasa a kasar ta Pakistan mai makamin nukiliya wanda ake ganin hakan bai rasa nasaba da rashin kyawun ababen more rayuwa.
Ko a Yunin 2021 sai da fasinjoji 63 suka rasu sakamakon hatsarin wasu jiragen kasa biyu bayan sun ci karo da juna a Sindh da ke Pakistan.