Wannan ne karo na biyu da ake kama fitaccen dan siyasar na Pakistan a bana. AFP

‘Yan sanda a kasar Pakistan sun kama tsohon firaiministan kasar Imran Khan a birnin Lahore da ke gabashin kasar.

Lauyansa ne ya tabbatar da batun kamun a ranar Asabar bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara uku a gidan yari kan zargin sayar da kayan gwamnati ba bisa ka’ida ba.

A ranar Asabar ne kotu ta yanke masa hukunci kan wata shari’a da ta shafi boye kadara, inda ake ganin hukuncin da aka yanke masa zai iya hana shi tsayawa takarar siyasa.

“Alkali Humayun Dilawar ya sanar da cewa hannun da yake da shi a cin hanci ya tabbata,” kamar yadda kafar watsa labarai ta Pakistan ta ruwaito.

Kotun Islamabad ta bayar da takardar sammaci domin kama Khan bayan samunsa da laifi, inda ‘yan sanda a Lahore suka yi gaggawa suka dauke shi daga gidansa zuwa babbar birnin Pakistan.

Hukuncin yana da alaka da binciken da hukumar zaben kasar ta gudanar wanda ta gano cewa Khan ya sayar da kadarorin gwamnati a lokacin da yake kan mulki a matsayinsa na firaiminista daga 2018 zuwa 2022.

Khan bai halarci zaman kotun da a aka yi a Babbar Kotun Islamabad ba inda alkalin ya bayar da umarnin kama shi.

Masana shari’a na ganin samun Khan da laifi zai sa ya kasa yin takara a babban zaben kasar da za a gudanar kafin watan Nuwamba.

Jam’iyyar Khan, Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) a wata sanarwa ta bayyana cewa tuni suka daukaka kara a Kotun Kolin kasar kan hukuncin da kotun gundumar kasar ta yanke.

Khan na fuskantar tuhume-tuhume sama da 150 tun bayan da aka hambarar da shi a Afrilun bara – zarge-zargen da yake cewa duk siyasa ce.

Tsohon dan wasan na kurket mai shekara 70 wanda ya koma dan siyasa, ana zarginsa da amfani da ofishinsa na firaiminista domin saye da siyar da kadarorin gwamnati da kasar ta samu kyautarsu a kasar waje wadanda kudinsu ya haura sama da dala 635,000.

TRT Afrika da abokan hulda