Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma a baya-bayan nan kungiyar ta'addanci ta Daesh reshen yankin ta kai hare-hare kan Jam'iyyar JUI-F. / Hoto: AA

Akalla mutane 44 ne suka mutu sannan fiye da 100 suka jikkata yayin wani harin kunar-bakin-wake da aka kai a wurin wani gangamin siyasa na jam'iyyar da aka fi goyon baya a arewa maso yammacin Pakistan, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Harin na ranar Lahadi da aka shirya kai wa jam’iyyar Jamiat Ulema-e- Islam- F (JUI-F) ta kawancen gwamnati da ke karkashin jagorancin wani fitaccen malamin addini, ya auku ne a daidai lokacin da daruruwan magoya baya suka taru karkashin wata rumfa a garin Khar da ke kusa da iyakar Afghanistan.

“Tantin ya fada kan mutanen da ke kokarin neman hanyar tsira,”a cewar Abdullah Khan, wani da ya yi kokarin taimaka wa wadanda lamarin ya rutsa da su.

"An shiga rudani sosai, inda gangar jikin mutane da gabobi da wasu sassan jiki suka tarwatsu ko’ina a wurin ga kuma gawarwakin mutane."

Sabeeh Ullah, dan kimanin shekara 24 da ke goyon bayan jam’iyyar, ya samu karaya a hannunsa, inda ya ce girman raunukan da mutane suka ji yana da matukar ban tsoro.

"Na tsinci kaina a kwance kusa da wani da ya rasa gabobin jinkinsa dukka, iskar da ake shaka a wajen ta cika da warin naman mutane," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillacin labarai AFP ta wayar tarho.

Yayin da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ke karuwa, Riaz Anwar -- ministan lafiya na lardin Khyber Pakhtunkhwa -- ya shaida wa AFP a yammacin ranar Lahadi cewa an tabbatar da mutuwar mutane 44 tare da jikkatar mutane 100.

"Harin kunar-bakin-wake ne, inda dan kunar-bakin-waken ya tayar da bam din da ke jikinsa a kusa da dandalin," kamar yadda ya shaida wa AFP.

Kafofin yada labarai na Pakistan sun ce akwai mutane kusan 400 a cikin tantin a lokacin da lamarin ya faru, kuma ma'aikatan bayar da agajin gaggawa da dama na ci gaba da aiki a wurin.

An yi ta yada hotunan wurin da harin ya auku a shafukan sada zumunta na intanet inda gawarwakin mutane da dama ke warwatse a kasa a ko'ina, kana masu aikin sa- kai suka rika taimaka wa wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa motocin daukar marasa lafiya.

Ana sa ran nan da ‘yan makonni masu zuwa za a rusa Majalisar Dokokin Pakistan gabanin zabukan da za a yi a watan Oktoba ko Nuwamba, kuma tuni jam’iyyun siyasa suke ci gaba da shirin yakin neman zabe.

Harin ya zo daidai da ziyarar da wata tawagar jami'an kasar China ke yi a kasar, ciki har da mataimakin firaministan kasar He Lifeng, wanda ya isa babban birnin Pakistan a yammacin ranar Lahadi.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi Allah wadai da harin yana mai jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suka aikata laifin.

Hare-hare kan malaman addini

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma a baya-bayan nan kungiyar ta'addanci ta Daesh reshen yankin ta yi ta kai hare-hare kan jam’iyyar JUI-F.

Ko a shekarar da ta gabata, Daesh ta dauki alhakin kai munanan hare-hare kan malaman addini da ke da alaka da jam'iyyar, wadda ta gina dimbin masallatai da makarantu a yankunan arewa da yammacin kasar.

Kungiyar ta'addancin ta zargi JUI-F da yin munafunci karkashin kungiyar addinin Musulunci wacce ke goyon bayan gwamnatoci da sojoji da suke adawa da su.

Shugaban jam'iyyar, Fazlur Rehman, ya shiga harkokin siyasa ne a matsayin mai tsattsauran ra'ayi, amma ya sassauta matsayarsa a tsawon shekaru a wani yunkuri na kulla kawance da jam'iyyu masu zaman kansu na hagu da dama.

Pakistan ta sha fuskantar hare-haren 'yan bindiga tun bayan da kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta karbe mulki a shekarar 2021.

TRT World