Kasashen Yamma na fargabar ziyarar Mista Kim Rasha za ta iya zama wata hanya ta kulla kawancen makamai. Hoto.Reuters

Kafofin watsa labarai na Rasha sun bayyana cewa Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na hanyarsa ta koma gida bayan ya kammala ziyarar da ya kai yankin Gabas mai nisa na Rasha.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha RIA ya bayyana cewa an gudanar da taron bankwana ga Shugaba Kim a ranar Lahadi.

Tun bayan da ya shiga Rasha a ranar Talatar da ta gabata, Mista Kim ya hadu da Shugaba Vladimir Putin inda kuma ya kai ziyara wasu muhimman wuraren soji da na kimiyya, wanda hakan ya jawo damuwa kan yiwuwar kasashen wadanda suka ware kawunansu su kulla alaka ta makamai.

Kafar watsa labarai ta Koriya ta Arewa ta yi bayani kan abubuwan da ziyarar Shugaba Kim ta mayar da hankali a kai inda ta ce ya gana da Ministan Tsaron Rasha Sergie Shoigu kan fadada dubaru da shirye-shiryen soji a tsakanin kasashen biyu.

Jami’an Amurka da Koriya ta Kudu sun bayyana cewa akwai yiwuwar Koriya ta Arewa za ta iya bai wa Rasha makamai kan yakin da take yi da Ukraine domin musayar wasu makamai na zamani da zai iya cika burin Shugaba Kim na samar da makamin nukiliya.

Duba makaman Rasha

Duka jiragen yakin Rasha da aka nuna wa Mista Kim na daga cikin wadanda aka rinka amfani da su sosai a yakin da ake yi da Ukraine, daga ciki har da Tu-160 da Tu-95 da Tu-22 wadanda jirage ne da suka yi fice wurin harba bama-bamai.

Shoigu, wanda ya hadu da Mista Kim a lokacin ziyarar da ya kai a Koriya ta Arewa a watan Yuli, ya kuma nuna masa wani sabon makami mai linzami na zamani mai suna hypersonic Kinzhal wanda ake saka wa jirgin yakin MiG-3.

Daga baya Mista Kim da Shoigu sun yi tafiya a ranar Asabar zuwa Vladivostok inda a nan ne suka duba jiragen ruwan yaki na Shaposhnikov frigate.

Kwamdandan sojin ruwa na Rasha Admiral Nikolao Yevmenov ya yi wa Mista Kim karin bayani kan irin ayyukan jirgin ruwan da makamansa, wadanda suka hada da makamai masu dogon zango da ke jikin jirgin wadanda aka rinka harba irinsu a cikin Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa wanda ya bayar da rahotanni kan ayyukan Shugaba Kim a Rasha ya bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin sojin shugaban sun raka shi ziyarar da ya kai a ranar Asabar, daga ciki har da ministan tsaronsa da manyan kwamandojin sojin sama da na ruwa.

AP