Akalla mutum 52 ne suka rasu sannan sama da 50 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin-wake da aka kai a taron Maulidi a lardin Balochistan na Pakistan, kamar yadda jami’an lafiya da ‘yan sanda suka tabbatar.
Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin wanda yake zuwa a daidai lokacin da ake samun karuwar hare-hare a yammacin kasar.
“Dan kunar-bakin-waken ya tayar da bam din ne kusa da motar mataimakin sufuritanda na ‘yan sanda,” kamar yadda Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda Munir Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ya kara da cewa an samu tashin bam din ne kusa da wani masallaci wanda mutane ke taruwa domin bikin Maulidi, wadda rana ce ta hutu.
Kungiyar Tehrik-e Taliban Pakistan mai ikirarin jihadi ta musanta kai wannan hari.
Ana yi wa wadanda suka jikkata magani a wani asibiti da ke garin Mastung wanda ke kusa da inda lamarin ya faru.
A watan Yuli, sama da mutum 40 ne suka rasu a harin kunar-bakin-wake a arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa a yayin wani taron addini.