0959 GMT — Adadin jariran da suka rasu sakamakon tsananin sanyi a tantunan Gaza cikin mako guda ya kai shida, kamar yadda wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Gaza ya sanar.
Ali al-Batran, wanda jinjiri ne da hare-haren Isra’ila suka sa iyayensa suka rasa matsuguninsu, ya rasu sakamakon tsananin sanyi da kuma ƙarancin ɗumi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hussaininsa, Jumaa al-Batran wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya a wani wurin kula da jarirai sabbin haihuwa a asibitin shahidai na al-Aqsa da ke Gaza, ya rasu sakamakon tsananin sanyi a ranar Lahadi.
Wannan mutuwar ce ta jawo adadin jariran da suka rasu sakamakon tsananin sanyi zuwa shida a makon da ya gabata.
2259 GMT — Sojojin Isra'ila sun tsare wasu Falasɗinawa marasa lafiya huɗu a lokacin da ake kan hanyar kai su Birnin Gaza daga arewacin Gaza domin yi musu magani, in ji ma'aikatar lafiya ta yankin.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce "dakarun mamaya sun tsare marasa lafiya hudu cikin 10 a yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tafe da su a hanya don karbar magani daga Asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza zuwa Asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza."
Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin ma'aikatan na cikin mawuyacin hali.
2334 GMT — Ministar Sadarwa na Isra'ila ya afka Masallacin Al-Aqsa
Ministan Sadarwa na Isra'ila Shlomo Karhi tare da rakiyar Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da suka mamaye yankunan Falasdinawa, sun afka masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye.
Karhi ya gudanar da ibada a daya daga cikin ramukan da ke karkashin bangon Yamma (bangon Al-Buraq) sannan ya yi tsokaci kan kutsen da aka yi wa X.
"A cikin wadannan kwanaki da sojojin Isra'ila ke samun nasara ta kowace fuska, na tuna da abin da Midrash (nassosin addini na Yahudawa) suka ce: 'A nan gaba, kofofin Kudus za su isa kofofin Damascus'.