An tura 'yan sanda kimanin 400  domin sanya ido a yankin. / Hoto: AFP

Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa wata babbar motar daukar kaya cikin taron jama'a a birnin New Orleans na jihar Louisiana a Amurka ya karu zuwa 15, a cewar jami'in da ke bincike kan sanadin mutuwa na New Orleans Dr Dwight McKenna.

"A halin da ake cikin mutum 15 ne suka mutu. Za a kwashe kwanaki da dama kafin gudanar da gwaje-gwaje kan gawawwakin dukkan mutanen. Da zarar an kammala gwaje-gwajen kuma mun tattauna da 'yan'uwan mutanen, za mu fitar da sunayensu,"in ji McKenna a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Tun da fari, an tabbatar da jikkatar mutum 35 bayan mutumin da ke cikin babbar motar daukar kaya ya kutsa cikin dandazon jama'a a unguwar French Quarter da misalin karfe 3.15 na safe (0915GMT) ranar Laraba.

Unguwar ta shahara saboda yadda masu yawon bude ido suke zuwa yankin domin gudanar da bukukuwan sabuwar shekara, musamman a jajiberen Sabuwar Shekara.

'Yan sanda sun ce mutumun ya tuka motar ta gefen hanya kusa da wurin da jami'an 'yan sanda suka ajiye motarsu inda ya mamayi jama'a ya kutsa cikinsu.

TRT World