Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 17 a hare-hare da suka kai ta ƙasa da ta sama a Gaza ranar Laraba da safe.  /Hoto: AA

Laraba, 1 ga watan Janairu, 2025

0526 GMT — Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 17 a hare-hare da suka kai ta ƙasa da ta sama a Gaza ranar Laraba da safe.

Isra'ila ta kai munanan hare-haren ne a ranar farko ta Sabuwar Shekara a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Bureij da ke tsakiyar Gaza da kuma garin Jabalia da ke arewa, a cewar kamfanin dillancin labarain Falasɗinu Wafa.

A cewar Wafa, wani jirgin helikwafta na Isra'ila ya kashe Falasɗinawa 15 — galibinsu ƙananan yara — a wani gida a Jabalia al-Balad.

A wani hari na daban, dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu yayin da suka kai hari ta sama a wani gida a Al-Bureij.

Kazalika, dakarun Isra'ila sun rusa wasu gidaje a garin Beit Lahia, da sansanin Jabalia da wasu gidaje da ke arewacin Gaza.

1958 GMT — Isra'ila ta riƙe gawawwakin Falasɗinawa 198 da ta kashe a 2024, in ji wata ƙungiya

Wata ƙungiya da ke fafutukar kare hakkin Falasɗinawa ta ce sojojin Isra'ila suna rike da gawawwakin Falasɗinawa 198 da suke kashe a shekarar 2024.

Ƙungiyar da ke ƙokarin ganin an karɓo gawawwakin mutanen da suka yi shahada mai suna National Campaign to Retrieve Martyrs' Bodies, ta ce, "hukumomin mamaya na Isra'ila suna riƙe da gawawwaki 198 na mutanen da suka yi shahada a 2024."

Ƙungiyar ta ƙara da cewa wannan adadi ɗaya ne bisa uku na gawawwakin mutum 641 da ke mutuware da "kaburburan da ba a yi wa lamba" na Isra'ila.

Waɗannan "kaburburan da ba a yi wa lamba" ba a rubuta sunan kowa a kansu ba saɓanin yadda ake yi wa gawawwaki.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a wani asibiti a Khan Younis / Hoto: Reuters

Ƙarin labarai 👇

2050 GMT — Hamas ta nemi a tsagaita wuta ta mako ɗaya — rahoto

Hamas ta nemi a tsagaita wuta ta mako ɗaya domin ta samu damar tattara bayanan 'yan Isra'ila da ake riƙe da su a yankin Gaza da aka mamaye, a cewar kafofin watsa labaran Isra'ila.

Hukumar Watsa Labaran Isra'ila Kan, ta ambato wasu majiyoyi daga ƙasar waje wadda ba ta faɗi sunansu ba suna iƙirarin cewa Hamas ta buƙaci a tsagaita wuta ba tare da ta gindaya wani sharaɗi ba, kamar sakin mutanen da ake tsare da su ko janye dakarun Isra'ila daga Gaza, ko kuma barin Falasɗinawan da aka kora daga gidajensu su koma arewacin Gaza.

A cewar kafar watsa labaran, Hamas za ta bayar da jerin sunayen da ake riƙe da su a kwana na huɗu na tsagaita wutar, kamar yadda Isra'ila ta buƙata, daga nan hukumomin Isra'ila za su yanke shawara kan su tsawaita tsagaita wutar ko su ci gaba da kai hare-hare.

2246 GMT — WHO ta kwashe majinyata 55 daga Gaza zuwa UAE

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta kwashe majinyata 55 da kuma masu kula da marasa lafiya 72 daga yankin Gaza zuwa Haɗaɗɗiyar Dalar Larabawa domin ba su kulawa ta musamman.

"Majinyatar sun haɗa da waɗanda suke fama da cutar autoimmune wadda garkuwar jiki take kai hari ga sassan jikin mutum bisa kuskure, da kansa da ciwon zuciya da ciwon ido da cututtukan da suka shafi lafiyar ƙwaƙwalwa da cutar fata," in ji WHO.

"Har yanzu majinyata fiye da 12,000 suna buƙatar a kwashe su daga Gaza," a cewar hukumar.

TRT World