Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025
1105 GMT — Akalla karin Falasdinawa 28 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza na Falasdinu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga watan Oktoban 2023 zuwa 45,581, in ji Ma’aikatar Lafiya a yankin.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 108,438 ne suka jikkata a harin da ake ci gaba da kai wa.
"Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 28 tare da jikkata wasu 59 a kisan kiyashi biyu na iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," in ji ma'aikatar.
"Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu hari," in ji ta.
0028 GMT — Isra'ila ta kashe mata da ƙananan yara a yankin da ake kira 'tudun-mun-tsira' na Gaza
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a wani hari da ta kai a tantin da wasu mutane da ta kora daga gidajensu suke samun mafaka a kudancin yankin Gaza da aka mamaye, a cewar ma'aikatan kiwon lafiya.
Mutanen 10, ciki har da mata da yara, sun mutu ne a tantin Al-Mawasi, wanda aka ayyana a matsayin wurin bayar da agaji ga mutanen da suke buƙatar agajin gaggawa a Khan Younis da ke yammacin Gaza, in ji jami'an asibiti.
Sun ƙara da cewa an jikkata mutum goma sha biyar.
Ƙarin labarai 👇
0009 GMT — Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasɗinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin Isra'ila sun buɗe wuta yayin wani samame da suka kai Tsohon Birnin Nablus da ke arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda suka jikkata mutum uku.
Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu ta ce an kai mutanen Asibitin Gwamnati na Rafidia da ke Nablus.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka jikkata ya samu munanan raunuka na harbin bindiga, yayin da biyu kuma suka samu ƙananan raunuka a ƙafa da cinya.