Jakadan Falasɗinu a Majalisar Ɗinkin Duniya Riyad Mansour ya zubar da hawaye yayin da yake karanto kalaman da wani likita daga ƙungiyar likitoci ta ƙasa da ƙasa Medecins Sans Frontieres, MSF, Mahmoud Abu Nujaila, ya rubuta a Asibitin Al Awda na Gaza kafin Isra'ila ta kashe shi a wani harin makami mai linzami a shekarar 2023.
Mansour ya shaida wa Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Juma’a cewa Nujaila ya rubuta a kan allon asibiti da ake amfani da shi wajen tsara tiyata cewa: “Duk wanda ya tsira har zuwa ƙarshe, zai ba da labari. Mun yi abin da za mu iya, ku tuna da mu.”
A cewar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta ƙasa da ƙasa da aka kafa a Dublin Front Line Defenders (FLD), Nujaila mai kare haƙƙin ɗan adam a Falasɗinu ne, likita, kuma ma'aikacin lafiya da yake aiki da ƙungiyar MSF.
A cewar FLD, "A lokacin yaƙin Isra'ila a Gaza a 2023, liktan yana kan gaba wajen jinyar waɗanda aka jikkata da waɗanda suka ji rauni, tare da sadukar da rayuwarsa a cikin yanayin kai munanan hare-hare."
A ranar 21 ga Nuwamba, 2023, an kashe Nujaila a wani harin da Isra'ila ta kai Asibitin Al Awda, tare da wasu likitoci biyu da masu kare haƙƙin bil'adama.
"Ya kasance a wurin yana jinyar marasa lafiya lokacin da aka kai hari hawa na uku da na hudu; asibitin na daya daga cikin sauran asibitocin da ke aiki a arewacin Gaza," a cewar FLD.
‘Ku kawo karshen wannan yakin’
Jakadan na Falasɗinu ya buƙaci kwamitin sulhun da ya kawo ƙarshen kisan kiyashin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza.
Ya ya yi wa taron Kwamitin Tsaron bayani kan irin halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, "Haƙƙi ne a kanmu baki ɗaya mu kawo ƙarshen wannan masifar, haƙƙi ne a kanmu mu kawo ƙarshen wannan kisan kiyashin.
"Kuna da alhakin ceton rayuka. Likitocin Falasdinawa da ma'aikatan kiwon lafiya sun saka wannan aiki a zuciyarsu duk da suna rasa rayuwarsu. Ba su yi watsi da waɗanda abin ya shafa ba. Ku ma kada ku yi watsi da su. Ku kawo ƙarshen cin karenta ba babbaka da Isra’ila take yi. Ku kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi. Ku kawo ƙarshen wannan cin zali nan take ba kuma tare da wani sharaɗi ba, yanzu," kamar yadda Mansour ya fada wa majalisar.
"Suna yakin da ba za su iya yin nasara ba, amma duk da haka ba sa son miƘa wuya," in ji shi.
A ranar Juma'a mambobin Kwaitin Tsaron na Majalisar Ɗinkin Duniya da dama sun bayyana damuwarsu kan mamayar da Isra'ila ke yi a asibitocin Gaza.
Jakadan Pakistan a Majalisar Ɗinkin Duniya Asim Iftikhar ya shaida wa Majalisar cewa "Kai hari da gangan ga ma'aikatan lafiya na asibitoci da marasa lafiya da waɗanda suka jikkata ya saɓa wa kowace ƙa'ida ta dokar jin ƙai kuma babu hujjar yin hakan."
Taron dai ya biyo bayan mamaye Asibitin Kamal Adwan da aka yi a makon da ya gabata da kuma tsare daraktansa Hussam Abu Safiya ba bisa ka'ida ba.
Yawan wadanda suka mutu ya zarce adadin da aka ruwaito?
Kisan kiyashin da Isra'ila ta yi a Gaza - wanda yanzu ke cikin kwanaki 456 - ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa sama da 45,658 tare da jikkata wasu sama da 108,583. A maƙwabciyarta Lebanon, Isra'ila ta kashe mutane 4,048 tun daga watan Oktoban 2023 kuma tana ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a ranar 27 ga watan Nuwamba.
Ana fargabar an binne Falasdinawa kimanin 11,000 a ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka kai harin. Wasu 10,000 kuma Isra'ila ta sace tare da kulle su a ɗakunan azabtarwa na Isra'ila.
Masana da wasu nazarce-nazarce sun ce wannan adadin ba shi ne ainihin na mutanen da aka kashe ba, amma ainahin adadin Falasiɗnawa da suka mutu zai iya kai wa kusan 200,000.
Yaƙin na Isra'ila ya haifar da ɓarna mai yawa tare da raba kusan kashi 90 cikin 100 na al'ummar Gaza miliyan 2.4 da mahallansu. Yanzu ana cikin yanayin sanyi, kuma dubban ɗaruruwan mutane suna fakewa a cikin tantuna kusa da teku.
Ana zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi ga Falasdinawa a Gaza a kotun ƙasa da ƙasa, yayin da kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ta bayar da sammacin kame manyan shugabannin Isra'ila ciki har da Firaministan Benjamin Netanyahu.