An samu ƙaruwar sojojin Isra'ila da ke kashe kansu tun bayan soma yaƙin Gaza

An samu ƙaruwar sojojin Isra'ila da ke kashe kansu tun bayan soma yaƙin Gaza

Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojin aƙalla 28 sun kashe kawunansu tun da aka soma yaƙi a Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta aƙalla 891 tare da jikkkata 5,569 tun bayan da aka soma yaƙin Gaza. /Hoto: AP

Sojojin Isra'ila aƙalla 28 ne ake tsammani sun kashe kansu tun da ƙasar ta kaddamar da yaƙin kisan ƙara-dangi a Gaza a watan Oktoba na shekarar 2023, a cewar rundunar sojin ƙasar.

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce ana tsammani sojoji 17 ne suka "kashe kawunansu" a shekarar 2024.

"Waɗannan alkaluma sun zarta na shekarar 2023 inda sojoji 17 ake zargi sun 'kashe kawunansu',' cikinsu har da guda bakwai da suka kashe kawunansu bayan ɓarkewar yaƙi," in ji sanarwar.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta aƙalla 891 tare da jikkkata 5,569 tun bayan da aka soma yaƙin Gaza.

Ta ce an kashe sojoji 363 a shekarar 2024, da kuma sojoji 558 a 2023, saɓanin sojoji 44 da aka kashe a 2022.

Kisan kiyashi

Rundunar sojin Isra'ila ta ce: "An buɗe layin wanda zai rika aiki babu dare babu rana domin bayar da shawarwari na kula da lafiyar ƙwaƙwalwa sannan an ƙara ma'aikata da ke lura da lafiyar ƙwaƙwalwa domin hana masu son kashe kawunansu."

Duk da ƙudurin da Kwamitin Tsaro na MDD ya yi wanda ya yi kira ga Isra'ila ta dakatar da buɗe wuta a Gaza, amma rundunar sojin ƙasar ta ci gaba da kai hare-hare na kisan kiyashi da suka kashe Falasɗinawa fiye da 45,600, galibinsu mata da yara, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023.

A watan Nuwamba da ya gabata, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da umarnin kama firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan Tsaron ƙasar Yoav Gallant bisa aikata laifukan yaƙi da na keta hakkin bil'adama a Gaza.

Kazalika Isra'ila tana fuskantar tuhuma game da aikata laifukan kisan kiyashi a Kotun Duniya kan yaƙin da take yi a Gaza.

TRT World