Mata suna jira don karbar abinci a cibiyar da ake rarraba wa Falasdinawan da suka yi gudun hijira a Deir al Balah, Gaza, Disamba 17, 2024. / Hoto: AP

Rayuwar da mata ke yi a sansanonin 'yan gudun hijira a Gaza na cike da ɗumbin wahalhalu da ƙasƙancin rayuwa, musamman ta wajen ɓoye sirrikansu na 'ya'ya mata kamar abin da ya shafi tsiraici.

Kullum ƙoƙarin mata shi ne su yi shiga ta kamala a tantunan da ke cike maƙil da dangi na kusa da na nesa da ma sauran mutanen da ba su sani ba, ciki kuwa har da maza.

Samun damar abubuwan buƙatar mata musamman a lokutan jinin al'adarsu yana wahala sosai, ta yadda sai dai su yi amfani da tsofaffin kaya ko tsumma wajen yin ƙunzugu.

Batun banɗaki kuwa yawanci ɗan rami ake tonawa a cikin yashi a ɗan zagaye shi da kwalaye, kuma a hakan ma, gomman mutane ne suke amfani da shi.

Alaa Hamami na fama ƙwarai da gaske wajen kiyaye darajarta inda ko yaushe take lulluɓe da wani baƙin mayafi da take sallah da shi, wanda ya rufe mata daga kanta har ƙasa.

"Yanzu kullum a cikin kayan da muke sallah muke, ko kasuwa za mu je shi muke sakawa," in ji matashiyar uwar mai 'ya'ya uku. "Daraja ta tafi."

A da ba ta saka wannan babban mayafin sai idan za ta yi kamsu salawati. Amma a yanzu da take rayuwa a inda mazan da ba muharramanta ba suke, dole ne ta dinga barinsa a jikinta ko yaushe, ko da kuwa bacci za ta yi — ko da a ce Isra'ila za ta kai hari inda suke ko kusa da nan da daddare to za ta iya tserewa ba tare da ɓata lokaci ba.

Yaƙin da Isra'ila ta shafe wata 14 tana yi a Gaza ya raba fiye da kashi 90 cikin 100 na Falasdinwa miliyan 2.3 da ke zaune a yankin da gidajensu.

A yanzu dubban mutane ne ke rayuwar ƙila-wa-ƙala cikin ƙazanta a sansanonin gudun hijirar da ke cike maƙil da jama'a.

Sharri da datti na kwarara a kan tituna, sannan da wahala ake samun abinci da ruwan sha. Ga sanyi yana ƙaruwa. Iyalai da dama a yanzu sai dai su yi ta maimaita kaya saboda sun bar kayan sawarsu a gidajensu lokacin da suke gudun ceton rai.

Kowa da kowa a sansanonin kalen abinci suke yi da ruwan sha da itacen girki a kullum. Rayuwar mata na tagayyare sosai.

"A da muna d agida cikin rufin asiri. A nan kuwa babu," in ji Hamami, wacce a yanzu mayafin sallar tata ma duk ya yayyage ya yi daƙa-daƙa da tokar itacen girki.

"A nan gaba ɗaya rayuwarmu babu sirri a cikinta. Mata ba su da sirri."

Ƙananan abubuwa ma wahalar samu suke yi

Wafaa Nasrallah, wata uwar 'ya'ya biyu d ake gudun hijira, ta ce ko 'yan ƙananan abubuwa da ba su kai sun kawo ba wahalar samu suke musu a rayuwar da suke yi a sansanin gudun hijira.

Ta yi ƙoƙarin amfani da 'yan ƙyallayen kaya haka ko ƙunzugun yara wato diaper, amma su ma sun ƙara tsada.

Banɗakin da take zuwa kuwa, ɗan rami ne aka haƙa aka zagaye shi da sanduna da bargo.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mata da yara 690,000 ne ke buƙatar kayayyakin kula da tsaftarsu musamman al'ada a Gaza, da kuma tsaftataccen ruwa da banɗakuna.

Ma'aikatan agaji ba sa iya cim ma buƙatun mutane, inda buƙatun ke ƙaruwa kuma ba a shigar da kayayyakin daga Isra'ila.

Babu kayayyakin kula da tsafta sannan farashinsu ya ƙaru sosai. Mata da yawa sai dai su haƙura da sayen ƙunzugun al'ada don su samu sayen abinci da ruwa.

Doaa Hellis, wata uwar 'ya'ya uku da ke zaune a sansanin gudun hijira ta ce tsofaffin kayanta take yagawa don ta yi ƙunzugun tare al'ada da su. "Duk inda muka ga ƙyalle to sai mun ɗauka mun yaga mun yi amfani da shi."

Ana sayar da fakitin audugar mata a kan shekel 45, kwatankwacin dala 12, "to mu ko shekel biyar ba mu da su a wannan tantin."

Wata ƙungiyar masu fafutuka mai suna Anera a Gaza, ta ce wasu matan sun koma shan maganin tsarin iyali don su dakatar da al'adarsu.

Wasu kuma tsarin zuwan jinin hailar tasu ya rikice saboda wahalhalu da kiɗima sakamakon yawan sauya wajen samun mafaka.

Wannan mummunan yanayi yana yi wa lafiyar mata barazana, in ji Amal Seyam, shugabar Cibiyar Kula da Harkokin Mata a Gaza, wadda ke samar wa mata kayan buƙatu da kuma tattara bayanai a kan halin da suke ciki.

Ta ce wasu matan sun shafe kwana 40 ba su sauya kayan jikinsu ba. Wannan abu da kuma rashin audugar mata mai kyau tabbas za su jawo musu cututtukan fara da na mahaifa da al'aura da ma taɓa lafiyar ƙwaƙwalwarsu, ta ce.

"Kwatanta yadda macen da ke Gaza ke ji, idan har ba ta iya shawo kan yanayin da ya shafi tsaftar jikinta da ta jinin hailarta ba," in ji Seyam,

Hellis ta tuna wani lokaci baya kaɗan, lokacin da kike jin dadin kawancewarki mace kuma babu wahalhalu sosai.

"A yanzu kayan sawa da bandaki da komai ma sun fi ƙarfin mata. An rikirkita tunaninsu," in ji ta.

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya kashe fiye da Falasdinawa 45,000, mafi yawansu mata da yara, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu.

Yayin da aka rugurguza mafi yawan biranen Gaza, daraja da ƙimar mata na ta zuewa saboda rayuwar na -ga-ta-kaina da suke yi a sansanonin gudun hijira.

Cikin taku kadan Hamami za ta iya zagaye tantin da suke rayuwa. Su 14 suke zama a wajen.

Ana tsaka da yaƙin ta haifi ɗanta aka saka masa suna Ahmed, wanda a yanzu watansa takwas.

Saboda lokacin da take shafewa wajen kula da 'ya'yanta uku da wanki da girki da ɗebo ruwa da sauran hidimar iyali, ta ce ba ta ma samun lokacin kula da kanta.

Akwai 'yan kayayyaki kaɗan da ke tuna mata rayuwarta ta baya, da suka hada da hodarta, wadanda ta kwaso daga gida a lokacin da take tserewa zuwa sansanin Shati a birnin Gaza.

Hodar dai ta barbaɗe. Amma ta ƙuƙuta ta ajiye wani ƙaramin madubi da take ta yawon sauya sansanoni da shi tun bara.

Madubin ma ya fashe gida biyu amma ta ƙi yasar da shi saboda tarihi.

"A da ina da kwabar ajiye kaya wadda ke ɗauke da abubuwa da dama da nake so," ta faɗa.

"Muna fita miƙe ƙafa kullum ko mu je liyafar biki ko suna ko zuwa wajen shaƙatawa don sayen duk abin da muke so."

Ta ce "mata sun rasa komai a wannan yaƙi. A da mata kan iya kula da kansu amma yanzu ba sa iyawa saboda an lalata komai."

TRT World