Wakilin Turkiyya a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen duniya da su gaggauta daukar matakin magance tashe-tashen hankula da rikici a Sudan.
Da yake jawabi a kwamitin sulhu a ranar Alhamis, Ahmet Yildiz ya yi tsokaci game da mummunan halin da ake ciki a Sudan, inda "fiye da mutum miliyan 11 suka rasa matsugunansu, dubbai kuma suka rasa rayukansu."
Rikicin ya kuma haifar da lalata muhimman ababen more rayuwa da suka hada da cibiyoyin lafiya.
Turkiyya ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da hadin kan kasar Sudan da 'yancin kan hana ƙasashen waje tsoma baki a lamarinsu.
Yildiz ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan musabbabin rikicin, inda ya yi kira da a gaggauta kawo karshen yakin.
"Don taimaka wa al'ummar Sudan, dole ne mu mayar da hankali kan musabbabin cutar, ba wai alamun cutar kadai ba," in ji shi, inda ya bukaci goyon bayan sanarwar Jeddah a matsayin wani muhimmin tsari na warware rikicin.
Turkiyya ta ƙara ƙaimi kan ayyukan jinƙai a Sudan, inda ta kai kusan tan 8,000 na kayan agaji ta jiragen ruwa guda uku zuwa Port Sudan.
Asibitin Turkiyya da ke Nyala na ci gaba da gudanar da aiki duk da mawuyacin halin da ake ciki, wanda ke nuna irin goyon bayan da Turkiyya ke bai wa al'ummar Sudan.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana aniyar Turkiyya ta taimaka wa Sudan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban majalisar mulkin Sudan Abdel Fattah al Burhan.
Yildiz ya ƙara da cewa, "Turkiyya ta jaddada goyon bayanta ga al'ummar Sudan tare da yin kira ga kasashen duniya da su ƙara ƙaimi wajen samar da agajin jinƙai da shiga tsakani."
Taron kwamitin sulhun ya jaddada bukatar hadin gwiwar kasashen duniya cikin gaggawa don daidaita Sudan da kuma hana ci gaba da zubar da jini.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023, Sudan ta fuskanci ƙazamin rikici tsakanin sojoji da dakarun Rapid Support Forces (RSF) game da sauye-sauyen soji da batun hadewar kasar.
Rikicin ya janyo asarar rayuka sama da 20,000 tare da raba miliyoyi da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na cikin mawuyacin hali na bukatar agajin jin kai a cewar MDD.