Hamas ta yi ikirarin cewa mayaƙanta sun yi garkuwa da ƴan Isra'ila da dama a wajen. Hoto: AA

Kungiyar Hamas ta harba dubban rokoki tare da tura gomman mayaƙa zuwa cikin yankunan 'yan kama-wuri-zauna na Isra'ila da garuruwan da ke kusa da Gaza, a wani lamari mai ban mamaki da ba a taɓa gani ba, da sanyin safiyar ranar Asabar din da ta zama ranar hutun Yahudawa.

Ga dai wasu muhimman abubuwa game da jerin hare-haren, waɗanda ba tare da ɓata lokaci ba suka jawo yaƙi tsakanin Isra'ila da Gaza.

Shin Isra'ila ta tsammaci harin?

Kaɗuwar da ƴan Isra'ila suka samu kansu a ciki a safiyar Asabar - ranar Simchat Torah, ɗaya daga cikin ranakun jin daɗi da hutu a kalandar Yahudawa - ta tuna wa mutane da abin mamakin da ya faru a shekarar 1973 na yaƙin Gabas ta Tsakiya, inda ƙasashen Larabawa suka samu wasu gagaruman nasarori.

Shekara 50 kafin wannan ranar, wani hari da Masar da Syria suka kai a ranar hutu ta Yahudawa, wacce a lokacin ta yi daidai da watan azumin Ramadana na Musulmai, nan da nan ya rikiɗe ya zama wani bala'i ga sojojin Isra'ila da aka shammata.

Don haka ya zuwa yanzu, ƴan Isra'ila sun yi amannar cewa ayyukan leƙen asirinsu zai bai wa sojojinsu damar ganewa idan za a kai musu wani babban hari ko kutse tun kafin ya faru.

Har yanzu waccar rashin nasarar tasu tana bibiyar Firaminista Golda Meir na wancan lokacin, tare da taimakawa wajen kawo ƙarshen mulkin Jam'iyyar Labour da ta daɗe tana sharafinta.

Yanzu, tambayar ta yadda aka yi ƙungiyar Hamas ta samu damar kai irin wannan tsararren babban hari - wanda tuni ya yi sanadiyar kashe ƴan Isra'ila da dama fiye da duk wani hari da aka taɓa kai wa tun bayan boren Falasɗinawa shekara 20 da suka gabata - sannan ba tare da barin fannin leƙen asirin Isra'ila ya gano komai ba, tuni ya zame wa gwamnatin Netanyahu ta masu kishin ƙasa wani babban ƙalubale.

Magoya bayan gwamnatin sun yi tsammanin Netanyahu da ministoci masu tsaurin ra'ayi da aka san su da aƙidar ƙin Larabawa, kamar su Ministan Tsaron Ƙasa Itamar Ben-Gvir, za su ɗauki wani mataki na rashin tausayi kan Falasɗinawa tare da mayar da martani fiye da yadda mayaƙan Gaza da aka yi wa ƙawanya suka yi.

A yayin da masu sharhi kan harkokin siyasa suka yi wa Netanyahu ca saboda gazawa, da kuma yadda yawan waɗanda suka mutu ke ƙaruwa, a lokaci guda Netanyahu na cikin barzanar rasa iko da gwamnatinsa da ma ƙasar baki ɗaya.

Ta yaya Hamas ta iya aiwatar da hare-harenta?

Hamas ta yi ikirarin cewa mayaƙanta sun yi garkuwa da ƴan Isra'ila da dama a wajen. Ta ce manyan dakarun soji na daga cikin waɗanda ta yi garkuwar da su.

Ba za a iya tabbatar da sahihancin bidiyoyin da ta sake ba, amma dai sun yi daidai da yanayin yankin.

A wani tashin hankali mai ban mamaki da ba a gani ba cikin gomman shekaru, Hamas ta kuma aike da lemominta na yaƙi masu tashi zuwa cikin Isra'ila, a cewar rundunar sojin Isra'ilan.

Wannan harin mai ban mamaki ya tuna da wani hari makamancinsa da ya faru a farkon shekarun 1980 lokacin da Falasɗinawa suka kutsa cikin arewacin Isra'ila daga Labanon a kan wata lema mai tashi suka kashe sojojin Isra'ila shida.

Bayan tsawon lokaci dai rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da sojoji da fararen hularta a Zirin Gazar da aka yi wa ƙawanya.

Me ya jawo faɗan?

Jami'an Hamas sun bayyana dalilai da suka haɗa da tsawon lokacin da suka ce Falasdinawa na fuskantar danniya daga Isra'ila, ciki har da ci gaba da dirarwa Masallacin Kudus, wanda ya kasance waje mai tsarki ga Musulmai.

Kudus, wanda kowanne ɓangare ke ikirarin nasa ne, Yahudawa waɗanda su ma sun ɗauke shi wajen bautarsu, suna kiransa da Temple Mount, kuma an sha yin rikici a kansa ciki har da wani mummunan hari da Isra'ila ta shafe kwana 11 tana kai wa a Gaza a shekarar 2021.

A shekarun baya-bayan nan, 'yan Isra'ila masu tsaurin ra'ayi irinsu Ministan Tsaron Ƙasa Ben-Gvir, suna yawan ziyartar masallacin.

A makon da ya wuce, lokacin bikin addini na Yahudawa da ake kira Sukkot, ɗaruruwan Yahudawa da ƴan Isra'ila masu kaifin kishin addini sun dirarwa wajen, lamarin da ya jawo Allah wadai daga Hamas da kuma zargin cewa Yahaudawa na ibada a wajen ne ta hanyar take dokar da aka cimma yarjejeniya a kanta.

Sanarwar da Hamas ta fitar ta kuma ba da misali kan yadda Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke ci gaba da mamayar yankunan Falasɗinawa da yadda Ben-Gvir ke ƙoƙarin tsaurarawa da takurawa fursunonin Falasɗinu da ke gidajen yarin Isra'ila.

A sasantawar da ake yi da Qatar da Masar da Majalisar Dinkin Duniya, Hamas na ta ƙoƙarin ganin Isra'ila ta amince da sauƙaƙa takunkumin shekara 17 da ta sanya wa Falasɗinu wanda ya jawo naƙasu sosai a harkokin tattalin arziki.

Wasu masu sharhi kan al'amuran siyasa sun alaƙanta rikicin da ake yi yanzu da tattaunawar da Amurka ta ƙaddamar ta ganin an sasanta tsakanin Isra'ila da Saudiyya.

Zuwa yanzu, rahotanni sun ce an sanya Falasɗinawan da ke Yammacin Kogin Jordan a cikin batun sasantawar, amma ban da na Zirin Gaza.

"Ko yaushe muna faɗa cewar sasantawa ba za ta sa da samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba," kamar yadda Bassem Naim, wani babban jami'in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

An fara yaƙin a lokacin da kawunan al'ummar Isra'ila ya rarrabu

An fara wannan yaƙin ne a lokaci mai tsauri ga Isra'ila, wacce take fuskantar jerin zanga-zanga mafiya girma a tarihinta kan ƙudurin Netanyahu na rage ƙarfin Kotun Ƙoli, a yayin da ake yi masa shari'a kan cin hanci.

Fafutukar zanga-zangar, wacce ke zargin Netanyahu da amfani da ƙarfin iko, tuni ta raba kan al'ummar Isra'ila tare da jawo rikici a tsakanin rundunar sojin ƙasar.

Ɗaruruwan sojojin ko-ta-kwana sun yi barazanar daina yin aiki a matsayin hanyar yin bore ga garambawul ɗin da ake son yi wa fannin shari'a.

Sojojin ko-ta-kwana su ne ƙashin bayan rundunar sojin ƙasar, kuma bore a cikin manyan sojoji ya jawo damuwa kan yiwuwar samun rashin goyon baya daga ɓangaren sojin.

An yi ta gudanar da jerin zanga-zangar duk mako tun daga farkon shekarar nan.

Wace matsaya ake tsammani?

Zuwa yanzu dai isra'ila ta ƙaddamar da manyan hare-hare huɗu a Gaza tare da harba rokoki a kan kungiyoyin da ke wajen.

A baya yarjejeniyar tsagaita wuta ta sha sa wa ana dakatar da yaƙi, amma a ko yaushe yarjejeniyar takan samu matsala.

Kowace yarjejeniya a baya takan samar da kwanciyar hankali na ɗan wani lokaci, amma a zahiri akwai matsalolin kutse da mamaya Israi'la ke ci gaba da yi a yankunan Falasɗinawa waɗanda ba a cika warware su ba, kuma hakan na janyo ci gaba da kai hare-haren sama da na rokoki.

Ganin irin salon da a wannan karon Hamas ta zo da shi, wataƙila ta matsa lamba a kan Isra'ila wajen amincewa da muhimman batutuwa, kamar sauƙaƙa takunkumai da sakin fursunoninta da ke tsare a Isra'ila.

TRT World