Sashen watsa labarai na Hezbollah ya saki wani bidiyo a ranar Litinin da ke nuna yadda ake harbin kyamarorin da suke wasu wurare biyar a iyakar Labanon da Isra’ila . Hoto: AA

1730 GMT — Shugabannin Tarayyar Turai za su yi taro don duba tasirin yakin ga Turai

Shugabannin Tarayyar Turai za su yi taron gaggawa ranar Talata, don duba damuwar da ke ƙaruwa kan cewa yaƙi tsakanin Isra’ila da kungiyar Falasɗinawa ta Hamas zai iya haifar da tashin-tashina a Turai tsakanin al’ummomi, kuma ya janyo karuwar ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka.

"Rikicin zai iya haifar da babban tasirin tsaro kan al’ummominmu," a cewar Shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Charles Michel, a wani taron ƙoli da aka gudanar ta bidiyo.

Taron da za a yi zai kuma mai da hankali kan samar da kayan agaji ga fararen hula, da aiki tare da sauran kasashen da ke yankin don dakatar da yaduwar rikicin.

1530 GMT — Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan yakin Isra’ila da Hamas

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai tattauna kan yakin Isra’ila da Hamas, yayin da rikicin ke shirin shiga matakin shigar dakarun kasa na Isra'ila zuwa Gaza.

Kwamitin ya ce zai fara tattaunawa da karfe 10 na dare agogon GMT.

Jami’an diflomasiyya sun ce akwai kudurori guda biyu da ake gogayyar gabatarwa: daya daga Rasha, wanda yake kiran tsagaita wuta da kai kayayyakin agaji zuwa Gaza, amma bai ambaci Hamas ba.

Dayan kuma Brazil ce ta shirya shi, wanda yake ayyana hare-haren Hamas na ranar 7 ga Oktoba wanda ya haifar da yakin a matsayin ta’addanci.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ya yi gargadin cewa Gaza tana fuskantar "mummunan hadari da rayuka" matukar ba a mayar da ruwa da sauran abubuwan buƙatar rayuwa da hukomomin Isra’ila suka katse ba.

15:00 Hezbollah ta lalata kyamarorin leken asirin Isra’ila a kan iyakar Labanon

Kungiyar mayaƙan sa kai ta Hezbollah ta Labanon ta ce ta fara lalata kyamarorin leƙen asirin da suke shingayen binciken sojin Isra’ila a kan iyaka, yayin da tashin hankali ke ta’azzara sakamakon ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke yi a Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.

Sashen watsa labarai na Hezbollah ya saki wani bidiyo a ranar Litinin da ke nuna yadda ake harbin kyamarorin da suke wasu wurare biyar a iyakar Labanon da Isra’ila, ta hanyar amfani da bindigogin da ake iya harbawa daga waje mai nisa.

Wani ɗan jaridar Reuters ya ce ga alama ƙungiyar na ƙoƙarin hana Isra’ila sa ido kan abubuwan da ke faruwa ne a ɓangaren iyakar Labanon, bayan da aka shafe kwanaki ana musayar wutar da ta jawo mutuwar mutum bakwai, ciki har da mayaƙan sa kai na Hezbollah hudu a ɓangaren Labanon din.

Kungiyar Hezbollah Logo

Isra’ila na ganin Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a matsayin barazana, inda ta ƙiyasta cewa Hezbollah tana da rokoki da makamai masu linzami 150,000 da take haƙon Isra’ila da su.

Akwai damuwar cewa ƙungiyar Hezbollah da take da matuƙar ƙarfi ka iya shiga yaƙin da Isra’ila, kuma a farkon watan nan Shugaban Amurka Joe Biden ya gargaɗi sauran masu ruwa da tsaki na Gabas ta Tsakiya da kar su shiga faɗan, sannan Amurka ta tura jiragen ruwa na yaƙi tare da shan alwashin goyon bayan Isra’ila.

14:30 Hamas ta harba makamai masu linzami Birnin Kudus da Tel Aviv

Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa Birnin Ƙudus da kuma Tel Aviv.

Rundunar Al Qassam a wata sanarwa ta ce ta kai harin ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa fararen hula a Gaza.

Tun da farko, rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kaurewar ƙarar jiniya a Tel Aviv da Birnin Ƙudus", manyan biranen Isra'ila, a yayin da Majalisar Dokokin kasar ke wani babban taronta na lokacin hunturu.

1400 — Netanyahu ya gargadi Hezbollah kan kai wa kudancin Isra'ila hari

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Iran da ƙungiyar Hezbollah da kar su ce za su taɓa shi a arewacin ƙasar.

Netanyahu ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra'ila ta Knesset, inda ya ce duniya na buƙatar haɗa kai don yin maganin ƙungiyar Hamas.

Netanyahu ya ce yaƙi da ƴan 'Nazi' wato Hamas yaƙi ne tsakanin rundunar haske da rundunar duhu.  Hoto: Others

Ya ce "wannan yaƙin kuma yaƙinku ne," sannan kuma ya ce Hamas da ƙungiyar Nazi tafiyarsu ɗaya.

Ya kara da cewa yaƙi da ƴan 'Nazi' wato Hamas yaƙi ne tsakanin rundunar haske da rundunar duhu.

"Mu za mu yi nasara, saboda a yanzu wanzuwarmu na cikin garari," kamar yadda Netanyahu ya shaida wa Knesset kan yaƙin da ƙasarsa ke yi da ƙungiyar Falasdinawa a Gaza.

1325 — Akwai yiwuwar Joe Biden zai tafi Isra'ila ranar Laraba

Ana sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai kama hanyar tafiya Isra’ila a ranar Laraba, kamar yadda tashar talabijin ta Isra’ila, Channel 12 ta ruwaito.

Sai dai babu wani tabbaci daga Fadar Shugaban Amurkar ko kuma gwamnatin Isra’ila kan ziyarar ta Biden.

A ranar Lahadi kafar watsa labaran ta Isra’ila ta ruwaito cewa Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika da goron gayyatarsa ga Shugaban Amurka domin ya kai ziyara Isra’ila domin nuna goyon bayansa ga kasar kan yakin da take yi.

1230 GMT — Shugaban Hukumar Jin-kai ta MDD zai tafi Gabas ta Tsakiya

Shugaban Hukumar Jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya bayyana cewa zai tafi Gabas ta Tsakiya a ranar Talata domin kokarin tattaunawa kan yadda za a kai kayan agaji Gaza.

A wani bidiyo da ya yi, ya bayyana cewa yana sa ran samun labari mai dadi a ranar Litinin kan batun kai kayan agaji Gaza.

“Muna neman hanyar kai agaji. Muna tattaunawa sosai da Isra’ila, da Masar da sauran kasashe,” kamar yadda Griffiths ya bayyana.

1020 Mata masu ciki 50,000 a Gaza ba sa samun isasshiyar kulawa - MDD

Hukumar Kidaya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai mata masu juna biyu kusan 50,000 a Zirin Gaza wadanda ba su samun kulawa ta lafiya.

Hukumar ta bayyana cewa mata masu ciki suna shan wahala wurin awon ciki haka kuma akwai kusan 5,500 wadanda ake zaton za su haihu a wannan watan.

Wakilin hukumar a Palestine Dominic Allen ya bayyana cewa shi kansa bangaren lafiya a Gaza na fuskantar barazana sakamakon hare-hare.

0855 — Isra'ila ta ce 'yan kasarta 199 ke hannun Hamas

Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun ce adadin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su sun karu zuwa 199 bayan harin da Hamas din ta kai.

Mai magana da yawun sojin na Isra’ila Daniel Hagari ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a yayin wata tattaunawa da kafofin watsa labarai.

A baya dai Isra’ila ta saka adadin kan mutum 155.

0755 — Adadin Falasdinawan da suka mutu ya kai 2,750

Adadin Falasdinawan da aka kashe sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza sun kai 2,750, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ta bayyana a ranar Litinin.

Adadin wadanda suka samu rauni ya karu zuwa 9,700.

A sanarwar da ta fitar a baya, ma’aikatar ta bayyana cewa sama da yara 750 na daga cikin mutanen da Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai.

Hukumomin lafiyan sun kuma bayyana cewa akwai mutum 58 wadanda suka mutu a Gabar Yamma da Kogin Jordan inda akalla mutum 1,250 suka samu rauni.

0720 — Sama da mutum miliyan daya sun gudu daga Gaza cikin mako daya

Akalla mutum miliyan daya suka gudu daga gidajensu a cikin mako guda daga Gaza, kamar yadda Hukumar Kula da Ayyukan Agaji ga Mutanen Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

“Akalla mutum miliyan daya aka tilasta musu barin muhallansu a cikin mako guda kadai. Dumbin mutane na ci gaba da tafiya zuwa kudanci,” kamar yadda UNRWA ta bayyana.

Hukumar ta kara da cewa babu wani amintaccen wuri da za a iya samun mafaka a cikin Gaza.

Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza kwana guda su bar birnin zuwa kudanci, sai dai kasashe da dama da kuma hukumomi sun bukaci Isra'ilar ta janye wannan matakin nata.

AA
AFP
Reuters