Hukumar Kula da Muhalli ta Birtaniya ta ba da gargadi mai tsauri game da raunin da Ingila ke da shi na fuskantar bala’in ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a cikin sabon hasashen kasa game da hadarin ambaliya (NaFRA), wanda ke nuna karuwar tasirin rikicin sauyin yanayi.
Cikakken rahoton da aka buga a wannan makon ya nuna cewa a halin yanzu kadarori miliyan 6.3 na cikin hatsari sakamakon ambaliyar ruwa da koguna da teku ke haddasawa.
Ana hasashen wannan adadi zai karu zuwa kusan miliyan 8 - ko daya cikin hudu - nan da shekarar 2050 yayin da ƙara samun hauhawar ruwan teku da matsanancin yanayi.
Ana dangata ambaliyar ruwan saman da mamakon ruwan sama da kuma gazawar magudanan ruwa a birane, wanda ke haifar da babban kalubale.
Adadin kadarorin da ke cikin hadarin sun haura zuwa miliyan 4.6, wata gagarumar karuwar kashi 43 cikin 100 daga ƙiyasin da aka yi a baya.
Nan da 2060, wannan hasashe na iya ƙaruwa zuwa miliyan 6.1 yayin da rikicin sauyin yanayi ke tsananta.
Zaizayar gabar teku, wani muhimmin abin damuwa, yana barazana ga kadarori 3,500 a yau, inda ake hasashen yawan zai ƙaru zuwa 10,100 a shekarar 2105 a ƙarƙashin Tsare-tsaren Gudanar da kula da gabar teku.
Rahoton ya ce "Jimillar kadarorin da ke yankunan da ke fuskantar hadarin zaizayar kasa za su ninka sau 9 a cikin lokacin har zuwa shekarar 2055, inda za su kai har zuwa 32,800."