1301 GMT — Netanyahu 'bai dace' da jagorantar Isra'ila ba: Tsohon Ministan Tsaro
Tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Benny Gantz ya ce Firaminista Benjamin Netanyahu "ba shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci Yahudawa ba."
"Netanyahu shi ne Firaminista, amma bai dace da jagorantar al'umma kamar al'ummar Isra'ila ba," in ji Gantz a shafin X.
Ya kara da cewa, kasar Isra'ila da al'ummar Isra'ila sun cancanci shugabanci na daban.
Netanyahu ya fuskanci kakkausar suka kan kin yin shawarwarin yarjejeniyar musayar fursunoni ga Isra'ilawa da ke tsare a Gaza da kuma zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa.
1054 GMT — Jami’an Falasdinawa sun zargi Yahudawa 'yan kama wuri zauna da ƙona masallaci a Yammacin Kogin Jordan
Jami'an Falasdinawa sun ba da rahoton cewa Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kona wani masallaci a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, lamarin da 'yan sandan Isra'ila suka ce ana gudanar da bincike.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu a Ramallah ta yi Allah-wadai da lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin "aiki na nuna wariyar launin fata a fili" da kuma nuni da "kamfen zuga jama'armu da wasu gungun 'yan ta'adda masu ra'ayin rikau na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suke aiwatarwa.
'Yan sandan Isra'ila da kuma hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet sun bayyana lamarin a matsayin wani lamari mai tsananin gaske.
Sun ce za su "dau matakin da ya dace don tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin", inda suka kara da cewa ana gudanar da bincike, tare da tattara shaidu daga wurin.
0351 GMT — Isra'ila na ci gaba da kai hari Gaza, ta kashe Falasɗinawa 19
Dakarun Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a sassa daban daban na Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 19 tare da jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da hukumar kiyaye farar hula ta Civil Defence ta fitar ta ce, an kai hare-hare ta sama a unguwar Sabra da ke kudancin birnin Gaza, inda aka auna gidajen iyalan Abu Shanab, Kiyyali da Al-Lawh, inda suka kashe mutum tara tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin lafiya sun ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan babura biyu a kudancin Gaza, inda suka kashe mutane uku.
Wani hari na daban da aka kai ta sama a tsakiyar birnin Gaza da kuma kudancin birnin Rafah ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Falasdinawa shida tare da jikkata da dama.
Kazalika, wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu a cewar rahotannin cikin gida.
0351 GMT — Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 10 a wani hari da ta kai kan sansanin al-Shati da ke Gaza
Akalla Falasdinawa 10 ne suka mutu, uku kuma suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza, in ji majiyoyin lafiya.
Sojojin Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawa da ke kan layin neman ruwa a sansanin, in ji majiyoyin.