Juma'a 4 ga Oktoban 2024
1237 GMT –– Isra’ila ta gano rokoki 100 da aka harba daga Lebanon tun da safiyar yau, inda wasu rokokin suka haddasa gobara a yankin Galili, a cewar tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra’ila.
Rokokin da kungiyar Hezbollah ta harba, sun kai ga jin ƙarar jiniya a arewacin Isra'ila.
Wasu harsasai sun sauka a budaddun wurare, lamarin da ya haddasa gobarar daji a sassan Galili, ko da yake ba a samu asarar rai ba.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Metula Settlement, David Azulai, ya bayyana cewa: "A kusan sa'o'i 24 da suka gabata, an samu labarin aukuwar makaman roka da harsasai guda 50 a Metula," a cewar jaridar Haaretz.
Azulai ya kara da cewa: "An samu gagarumar barna ga gidaje, wuraren wasa da dandali, da muhimman ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da ruwan sha."
0952 GMT –– Khamenei na Iran ya ce harin da Iran ta kai Isra'ila halal ne kuma mai inganci
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Khamenei ya ce harin makami mai linzami na baya-bayan nan da Iran ta kai kan Isra'ila "abu ne da aka shirya masa kuma halal ne" kuma shi ne mafi karancin hukuncin "laifukan" Isra'ila.
A cikin jawabinsa na mintuna 40 ga dubban jama'a a Masallacin Mosalla, babban wurin addu'a a birnin Tehran, Khamenei ya ce harin da Hamas ta kai kusan shekara guda da ta gabata a ranar 7 ga Oktoba, 2023, matakin da al'ummar Falasdinu suka dauka ne.
Ya kuma ce Iran ba za ta yi jinkiri ba kuma ba za ta yi gaggawar aiwatar da aikinta na tunkarar Isra'ila ba, ya kara da cewa harin makami mai linzami da aka kai kan Isra'ila yana bisa doka.
Iran ta harba makami mai linzami kan Isra'ila a ranar Talata a wani matakin da ta ce na ramuwar gayya ne kan harin da Isra'ila ta kai a Beirut da ta kashe shugaban Hizbullah Nasrallah a ranar Juma'ar da ta gabata da kuma kisan gillar da aka yi wa shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran a watan Yuli.
2100 GMT — Amurka ta goyi bayan mamayar Isra'ila a Lebanon yayin da ake ci gaba da kai hare-hare Beirut
Gwamnatin Biden ta yi imanin cewa ya dace Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama kan kasar Lebanon a halin yanzu, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller, duk da cewa ya amince da hatsarin mamaye Lebanon din ya zarce manufofin Isra'ila a halin yanzu.
Isra'ila ta aike da dakaru zuwa kudancin Lebanon a wannan makon bayan wani ƙazamin hari ta sama da aka kai tsawon makwanni biyu a cikin wani mummunan rikici da ya janyo Iran da kuma hadarin saka Amurka.
Da yake magana a wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Miller ya ce yanayin duk rikice-rikicen, ba za a iya tantance shi ba, don haka ba zai yiwu a fadi tsawon lokacin da Isra'ila za ta dauka ba wajen cimma burin da ta bayyana na kawar da ababen more rayuwa na Hezbollah a kudancin Lebanon, tare da ba da dama domin mayar da ‘yan Isra’ila da aka kora daga gidajensu da ke kan iyaka ta hanyar harba rokoki tsawonawatanni.
2130 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 37 a Lebanon cikin sa'o'i 24
Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta fitar ta ce Isra'ila ta kashe akalla mutum 37 tare da jikkata wasu 151 a hare-haren da ta kai a fadin kasar Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A halin da ake ciki kuma, makami mai linzamin na Isra'ila ya kai hari a gefen filin jirgin saman Beirut, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Har ila yau Isra'ila ta kai hare-hare a yankunan kudancin Beirut "sau 11 a jere", in ji kamfanin dilancin labaran AFP, yana mai cewa an ji ƙarar jiniya kuma gine-gine sun girgiza a babban birnin Lebanon.