Shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Talata ya sa hannu kan wata doka da aka sabunta kan makaman nukiliya, wadda ta bai wa Moscow damar amfani da makamin a matsayin martani kan wata ƙasa da ba ta da ƙarfin nukiliya, ta samu goyon baya daga kasashe masu ƙarfin nukiliya ta kai mata hari.
"Ya zama dole mu daidaita ƙa'idojinmu da yanayin halin da ake ciki yanzu," kamar yadda mai magana da yawun Kremlin Dmitry Peskov ya shaida wa manema labarai.
Matakin sauya dokar nukiliyar Rasha, martani ne da Kremlin ta bayar ga rahoton matakin gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta dauka na bai wa Ukraine damar harba makamai masu linzami masu cin dogon zango na Amurka a Rasha.
Matakin ya biyo bayan kaiwa rana ta 1,000 na yakin Rasha da Ukraine.
Dokar wadda aka sabunta, ta bayyana barazanar da aka iya sanya Rasha mayar da martanin harin nukiliya, kamar hare-haren da makamai masu linzami ko jirage marasa matuƙa ko wasu jiragen sama.
Sauye-sauyen dokar nukiliya
Kazalika dokar ta bayyana cewa, duk wani matakin wuce gona da iri kan Rasha daga wani mamba na ƙawancen, Moscow za ta dauki shi a matsayin wani hari daga dukkan bangarorin kawancen.
Makonni kaɗan gabanin zaben shugaban ƙasar Amurka a watan Nuwamba, Putin ya buƙaci a samar da sauye-sauye kan dokar nukiliyar ƙasar kan cewa duk wani hari aka kai kan Rasha da taimakon kasashen masu makaman nukiliya za a dauƙe shi a matsayin harin haɗin gwiwa kan Rasha.
Yakin Ukraine na tsawon shekaru biyu da rabi ya haifar da mummunan rikici tsakanin Rasha da Amurka tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuban a shekarar 1962 - wanda ake ganin shi a matsayin yakin cacar baka mafi kusa da manyan ƙasashen biyu suka yikin makami mai linzami.