Shugaban kungiyar sojojin haya ta Wagner Yevgeny Prigozhin ya umarci dakarunsa su tattara karfinsu zuwa ga Afirka.
Ya bayyana haka ne a wani bidiyo da aka watsa wanda ya nuna shi yana yi wa dakarunsa maraba da zuwa Belarus, tare da shaida musu cewa daga yanzu ba za su kara fafatawa a yakin Ukraine ba.
Kasashen Yamma sun bayyana rashin nasarar tawayen kungiyar Wagner na ranakun 23 da 24 ga watan Yuni a matsayin kalubale ga mulkin Shugaba Vladimir Putin.
Sun ce hakan ya nuna raunin shugaban mai shekaru 70 da kuma tasirin yakin da Ukraine ke yi a kan Rasha.
Bidiyon, wanda aka watsa a shafin Telegram ranar Laraba, shi ne shaida ta farko da ta nuna inda Prigozhin yake tun daren da kungiyarsa ta yi bore.
A cikin bidiyon, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kasa tantance sahihancinsa a nan take, an jiyo wani mutum da muryarsa ta yi kama da ta Prigozhin yana yi wa dakarunsa maraba.
"Barka da zuwa, 'yan samari ... Barkanku da zuwa kasar Belarus," in ji Prigozhin.
"Mun fafata cikin mutunci," in ji Prigozhin. "Kun yi wa Rasha babban aiki, abin da ke faruwa a gaba abin kunya ne da ba ma bukatar mu sanya kanmu a ciki."
Da farko dai Putin ya ce zai murkushe 'yan tawayen, inda ya kwatanta lamarin da ya faru da rikicin da ya haifar da juyin juya hali na shekarar 1917.
Bayan wasu sa’o’i ne aka kulla yarjejeniya da Prigozhin da wasu mayakansa don su tafi Belarus.
Tun bayan nan ne, aka yi wa Prigozhin ganin karshe yana barin birnin Rostov na kasar Rasha a ranar 24 ga watan Yuni.
A yanzu dai ba a san abin da kungiyar Wagner wacce Prigozhin ya ce tana da mayaka 25,000 za ta yi ba.
Sai dai Prigozhin ya nemi dakarunsa da su kasance masu kyakkaywar dabi'a ga mutanen kasar sannan ya bukaci su horar da sojojin Belarus kana su tattara karfinsu don yin "sabuwar tafiya zuwa Afirka."