#GWP85 : Putin's 'chef' Prigozhin sues EU over sanctions / Photo: AFP

Yevgeny Prigozhin, shugaban kungiyar sojojin haya ta Wagner, ya yi kira da a yi tawaye domin kifar da Ministan Tsaron Rasha.

Nan take Moscow ta mayar da martani ta hanyar kaddamar da bincike na aikata laifuka kan Prigozhin.

A baya ya soki shugabannin sojin kasar bisa gazawarsu a yakin Ukraine kuma ya yi kaurin-suna wajen samu rashin jituwa da Ma'aikatar Tsaron kasar.

Mun yi nazari kan Prigozhin, mai shekarau 62 da kuma rawar da kungiyarsa ta Wagner ta taka a yakin.

Me Prigozhin ya ce?

Prigozhin ya wallafa wasu bidiyoyi da sakonnin murya cikin fushi inda ya zargi Ministan Tsaro Sergei Shoigu da bayar da umarnin kai hari da makaman roka kan sansanin mayakan Wagner da ke Ukraine ranar Juma'a, inda dakarunsa ke taya Rasha yaki.

Prigozhin ya ce dakarunsa za su hukunta Shoigu a wani bore na soji sannan ya yi kira ga sojojin kasar kada su mayar masa da martani.

"Wannan neman yin adalci ne, ba juyin mulkin soji ba,'' in ji Prigozhin.

Ma'aikatar Tsaron ta musanta kai hari da makaman roka kan sojojin haya na Wagner.

Kwamitin Kasa da ke Yaki da Ta'addanci, wanda bangare ne na Hukumar Tsaro ta Kasa ko FSB, ya ce zai bincike shi saboda kiran da ya yi a yi bore.

FSB ya yi kira ga sojojin haya na Wagner su kama Prigozhin kua kada su bi "umarninsa na aikata laifi da yaudara."

Ya bayyana kiran da shugaban sojojin hayar ya yi a matsayin "yi wa dakarun Rasha yankan-baya" sannan ya ce hakan tamkar kira ne a dauki makamai domin yi wa Rasha bore.

'Yan sandan kwantar da tarzoma da Zaratan Sojoji sun tsaurara tsaro a wurare na musamman a Moscow, ciki har da gine-gine gwamnati da hukumomi da wuraren sufuri, kamar yadda Tass ya rawaito.

Tarihin Prigozhin

A 1981 an zartar wa Prigozhin hukunci kan laifin fashi da makami da kai hari, sannan aka yanke masa hukuncin daurin shekara 12 a kurkuku.

Russia's Prigozhin posts first video since mutiny, hints he's in Africa

Bayan an sake shi, ya bude gidan sayar da abinci a birnin St. Petersburg a shekarun 1990.

Ta wannan hanya ce ya gamu da Shugaba mai-ci Vladimir Putin, wanda a wancan lokaci shi ne mataimakin magajin birnin.

Prigozhin ya yi amfani da sanayyarsa wajen bunkasa sana'ar sayar da abinci inda ya samu kwangiloli masu tsoka a wurin gwamnatin Rasha har ma aka yi masa lakabi da "mai dafa abincin Putin."

Daga bisani ya sanya hannunsa a wasu sana'o'i, cikinsu har da bude gidajen watsa labarai da kuma shararriyar sana'arsa ta "kamfanin cin zarafin mutane" a intanet lamarin da ya sa Amurka ta tuhume shi da tsoma baki a zaben shugaban kasar na 2016.

A watan Janairu, Prigozhin ya amince cewa ya kafa kungiyar sojojin haya ta Wagner.

A wadanne wurare ne Wagner ta yi ayyuka?

An soma ganin sojojin Wagner a gabashin Ukraine ba da jimawa ba bayan rikicin ‘yan aware da ya barke a Afrilun 2014, makonni bayan da Rasha ta kwace iko da yankin Crimea na Ukraine din.

Duk da cewa ta goyi bayan ‘yan aware a Donbass, wanda shi ne zuciyar masana’antu da ke gabashin Ukraine, Rasha ta musanta tura makamanta da dakarunta can duk da wasu hujjoji da ke da akwai a kasa.

Hadawa da sojojin haya a rikicin ya bai wa Moscow damar ci gaba da musanta lamarin.

Ana kiran kamfanin Prigozhin da suna Wagner inda aka rada wa kamfanin inkiyar sunan kwamandansa na farko wato Dmitry Utkin, wani kanal mai ritaya na rundunar soji ta musamman ta Rasha.

Ba da dadewa ba sojojin na Wagner suka yi kaurin suna wurin rashin imani a yakin da suke yi. An tura sojojin na Wagner zuwa Syria inda Rashar ta goyi bayan Bashar Assad a yakin basasa.

A Libiya kuwa, sun taya Khalifa Haftar yaki. Haka kuma sojojin sun yi aiki a Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Mali.

Rahotanni sun nuna cewa Prigozhin ya yi amfani da zuwan dakarunsa Syria da kuma kasashen Afirka domin samun lasisin hakar ma’adinai.

Daya daga cikin sakatarorin harkokin wajen Amurka Victoria Nuland a watan Janairu ta bayyana cewa kamfanin na amfani da gwala-gwalan da yake samu a Afirka domin daukar nauyin yakin Ukraine.

Wasu daga cikin kafafen watsa labarai na Rasha sun yi zargin cewa Wagner na da hannu a kisan ‘yan jaridar Rasha uku a 2018 wadanda ke bincike kan ayyukan kungiyar a Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka.

Wane tarihi Wagner ta kafa?

Kasashen Yamma da kuma kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya sun sha zargin sojojin hayar Wagner da take hakkin bil adama a fadin Afirka a kasashe da suka hada da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Libya da kuma Mali.

A 2021, Kungiyar Tarayyar Turai ta zargi rundunar da “tsananin cin zarafin bil adama, ciki har da kisa ba bisa ka’ida ba,” da gudanar da “ayyukan tayar da rikici” a Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Libiya da Ukraine.

Akwai wasu bidiyo wadanda ake zargin sojojin na Wagner ne inda suke gudanar da abubuwan da ke bata darajar sojin.

Wani bidiyo na shekarar 2017 ya nuna gungun mutane dauke da bindiga wadanda ake zargin na Wagner din ne suna azabtarwa da kuma dukan wani dan Syria da guduma har suka kashe shi, inda suka daddatsa jikinsa da kuma kona gawarsa.

Hukumomin Rasha sun yi watsi da bukatar kafafen watsa labarai da masu kare hakkin bil adama domin gudanar da bincike.

A 2022, wani bidiyo ya nuna wani tsohon sojan Wagner ana dukansa har ya mutu da guduma bayan an zarge shi da komawa bangaren ‘yan Ukraine inda aka tasa keyarsa.

Duk da yadda jama’a suka nuna bacin ransu da kuma bukatar gudanar da Bincike, fadar Kremlin ta kawar da kanta kan lamarin.

AP