Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024
1420 GMT –– Shugaban kungiyar Hezbollah Naim Qassem ya fada a wani jawabi da aka watsa cewa, mayar da martani ga kazamin harin da Isra'ila ta kai a birnin Beirut na baya-bayan nan zai kasance a tsakiyar Tel Aviv.
"Dole ne a sa ran mayar da martani a tsakiyar Tel Aviv," in ji Qassem, bayan wasu munanan hare-hare da aka kai a wasu gundumomi uku na tsakiyar birnin Beirut a 'yan kwanakin nan, wanda daya daga cikinsu ya kashe mai magana da yawun Hezbollah Mohammed Afif da wasu 'yan tawagarsa guda hudu.
0830 GMT –– Sojojin Isra'ila sun shiga kwana na biyu suna luguden wuta a birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin Isra'ila sun shiga kwana na biyu suna luguden wuta a birnin Jenin da yankuna da ke gefensa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Kafofin watsa labaran yankin sun ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kai samame a gidajen da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jenin tare da tsare mutane da dama, ciki har da wata mata.
A yayin da wannan cin-fuska na Jenin ya shiga kwana na biyu, rundunar sojin Isra'ila ta tura ƙarin sojoji da motocin buldoza zuwa yankin.
Adadin Falasɗinawan da aka kashe a birnin daga ranar Litinin zuwa yau ya kai biyar, a cewa wasu majiyoyi daga asibiti.
2300 GMT — Isra'ila ta kai hari da bama-bamai a Gaza, Falasɗinawa 20 sun mutu ko sun ɓata
Jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden bama-bamai a gidan wani mutum mai suna Joudeh da ke Tsohon Titin Gaza a yankin Jabalia al-Balad na arewacin Gaza, inda Falasɗinawa 20 suka mutu ko kuma suka ɓata, a cewar wasu ganau da kuma rahotanni daga yankin.
Kafofin watsa labaran yankin sun ce mutum 12 sun mutu sakamakon luguden wutar da jiragen yaƙin Isra'ila suka yi.
Cibiyar samar da bayanai kan Falasɗinawa ta Palestinian Information Center, ta ce mutum 10 sun ɓata.
A gefe guda, an jikkata wani ɗan jaridar Gaza Hossam Shabat wanda ke jerin manema labarai da Isra'ila take so ta kashe, kamar yadda Shabat ya wallafa a shafinsa na X.
"A daren nan, dakarun Isra'ila sun kawo mini hari da gangan. Bayan na samu labarin tashin bam a maƙotanmu, na tsere cikin motata domin bayar da rahoto. Lokacin da na isa gidan da lamarin ya faru, na ga mutane a kiɗime suna ihu domin neman agaji daga hawa na biyu na ginin," in ji shi.
"Lokacin da na shiga gidan, an sake kai masa hari inda wasu sassan jikin mutane suka faɗo kaina. Ɓuraguzai sun faɗo a kaina da kuma kan abokan aikina. An kashe ɗaya daga cikin mutanen da suka soma isa gidan yayin da ni da wani abokin aikina muka jikkata, kuma wasu da dama sun riga mu gidan gaskiya."
2300 GMT — Hezbollah ta harba wa sojojin Isra'ila 'taƙaitattun makamai masu linzami'
Hezbollah ta ce ta harba makamai masu linzami ga wasu dakarun Isra'ila da suka je yin mamaya a yayin da suke kwashe abokan aikinsu da aka jikkata da waɗanda aka kashe a kudancin Lebanon.
A wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ta Hezbollah ta ce ta jikkata sojojin Isra'ila a harin da ta kai musu da makamai masu linzami a kan iyakar garin Markaba sannan ta harbi wasu sojojin da suka je domin kai musu ɗauki.
Kazalika Hezbollah ta ce ta harba wani makami mai linzami kan "bataliya ta uku" da ta je domin "kwasar sojojin da suka jikkata da waɗanda suka mutu".