Alhamis, 21 ga Nuwamban 2024
1133 GMT –– Yawan mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 13 tana yi a yankin ya haura 44,000, in ji jami’an kiwon lafiya na yankin.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce fiye da rabin wadanda suka mutu mata ne da kananan yara.
Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta ce mutane 44,056 aka kashe yayin da 104,268 suka samu raunuka tun farkon yakin.
Ta ce adadin wadanda suka mutu ya zarta haka saboda dubban gawarwakin da aka binne a karkashin baraguzai ko kuma wuraren da likitoci ba za su iya shiga ba.
0415 GMT — Gidajen burodi bakwai ne kawai ke aiki a Gaza na Falasdinu: MDD
Da yawa daga cikin gidajen burodi a Gaza sun rufe saboda karancin kayan abinci da ake bukata don yin biredi, kamar fulawa da mai, in ji kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric.
Ya kara da cewa sauran gidajen burodin kuma suna fuskantar rufewar nan kusa, yana mai cewa a halin yanzu gidajen burodi bakwai ne kawai a Gaza da aka yi wa ƙawanya ke aiki tare da tallafi daga kungiyoyin agaji.
"Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sassa na arewacin Gaza ke fuskantar barazanar yunwa," in ji Dujarric, yana mai nuni da cewa an samu karuwar matsananciyar yunwa a tsakiya da kudancin Gaza.
2245 GMT — Isra'ila ta kashe akalla Falasdinawa 66 tare da raunata wasu 100 a wani sabon kisan kiyashi da aka yi a wani gida da ke kusa da Asibitin Kamal Adwan a arewacin Gaza, kamar yadda 'yan jarida da shaidun gani da ido suka bayyana.
Wani dan jaridar Falasdinawa Hossam Shabat ya ruwaito cewa, harin bam din ya halaka iyalan Al-Madhoun, da Khader, da Abu Wadi, da Shaqoura, da kuma Nassar, inda ya ce, "Harin mai ban tsoro ya shafi iyalai da dama da suka rasa matsugunansu."
Hussam Abu Safiya, Daraktan Asibitin Kamal Adwan ya shaida wa manema labarai cewa, akwai mutum 200 a wurin da aka yi kisan kiyashin, tare da dimbin “Shahidai, da suka samu raunuka da kuma waɗanda ba a gani ba” har yanzu a karkashin baraguzan gidajen da aka kai harin.
Ya ce ma’aikatan kiwon lafiya na ci gaba da ceto wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin wadanda Isra’ila ta kashe, inda ya kara da cewa asibitin ba shi da motocin daukar marasa lafiya da za su kai wadanda suka mutu asibiti sakamakon kisan kiyashin Isra’ila.
A halin da ake ciki kuma, adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan gidan iyalan Al-Arouqi da ke unguwar Sheikh Radwan ya kai 22, ciki har da kananan yara 9, in ji jami'ai.
2158 GMT - Shugaban Hezbollah ya ce sulhu na hannun Netanyahu
Shugaban kungiyar Hezbollah Naim Qassem ya ce kungiyarsa ta mika ra'ayoyinsu kan shawarar da Amurka ta gabatar na kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi wa kasar Labanon, yana mai cewa a halin yanzu yarjejeniyar ta ta'allaka ne kan martanin Isra'ila da kuma "muhimmancin" da Firaminista Benjamin Netanyahu zai ba ta, wanda yake daƙile yin sulhu a Gaza tsawon watanni 13 da suka gabata.
A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, Qassem ya yi nuni da tsayin dakan da kungiyar Hezbollah ta yi a fagen daga, yana mai cewa kungiyar a shirye take ta yi mummunar asara kan sojojin Isra'ila da suka mamaye.
Ya kuma bayyana karara cewa kungiyar Hezbollah ba ta dakatar da yakin ba yayin da take jiran sakamakon shawarwarin.
Qassem ya ce, "Mun karbi takardar shawarwarin, mun yi nazari sosai tare da bayar da ra'ayoyinmu," in ji Qasem, inda ya kara da cewa, kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri shi ma yana da ra'ayi, wanda ya yi daidai da matsayin Hezbollah.
"An gabatar da wadannan kalamai ga wakilin Amurka Amos Hochstein kuma an tattauna dalla-dalla."
Qassem ya jaddada cewa, Hezbollah za ta daina tattauna takamaimiyar yarjejeniyar da aka cimma, har sai an ci gaba da tattaunawa cikin kwanciyar hankali.
An fara nuna damuwa a Lebanon game da yuwuwar bukatun Isra'ila, musamman dangane da bukatar da Isra'ila ke da ita na 'yancin walwala ga sojojin Isra'ila a Lebanon.