Talata, 19 ga watan Nuwamba, 2024
1024 GMT — Fiye da yara 200 aka kashe a Lebanon cikin watanni biyu da suka gabata — UNICEF
Fiye da yara 200 ne aka kashe tare da jikkata 1,100 a Lebanon cikin watanni biyun da suka gabata, in ji kakakin Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).
“200 da aka kashe din a cikin watanni biyu da suka gabata ne kawai. Aƙalla 231 aka kashe tun farkon yaƙin a bara,” James Elder ya shaida wa taron manema labarai na Geneva a matsayin amsa ga tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa game da asarar rayukan da aka samu.
Sai dai bai ce ko wane ne ke da alhakin kisan ba, yana mai cewa a bayyane yake ga duk mai bibiyar kafafen yada labarai.
0643 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila a Tel Aviv
Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai wa sojojin Isra'ila hare-hare ta sama a Tel Aviv.
A wata sanarwa da ta fitar, Hezbollah ta ce harin, wanda ta kai ranar Litinin da maraice da jiage marasa matuƙa da yawa, ya lalata harkokin sojin Isra'ila Tel Aviv, babban birnin ƙasar.
Sai dai ba ta yi ƙarin bayani ba kan harin, ko da yake daga bisani ƙungiyar ta ce za ta yi bayani dalla-dalla kan wuraren da ta kai harin a Isra'ila.
Ranar Litinin da maraice, jaridar Israel Hayom ta ruwaito cewa rokokin da aka harba daga Lebanon sun faɗa kusa da wani babban kanti a birnin Ramat Gan da ke gabashin Tel Aviv, lamarin da ya haddasa tashin gobara, yayin da kafar watsa labarai ta Channel 12 ta bayar da rahoton jikkatar mutum biyar.
Kazalika jaridar Yedioth Ahronoth ta ce an dakatar da aiki a filin jirgin saman Ben Gurion sakamakon harin.
0021 GMT –– Shugabannin ƙasashen G20 sun yi kira a aiwatar da 'gagarumin' shirin tsagaita wuta a Gaza da Lebanon
Shugabannin ƙasashe na ƙungiyar G20 sun yi kira a aiwatar da "gagarumin" shirin tsagaita wuta a Gaza da Lebanon a wata sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar a wurin taronsu a Brazil ranar Litinin.
Shugabannin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki na duniya sun yi kira a aiwatar da shawarwarin Amurka na daina buɗe wuta a yankin Gaza na Falasɗinu tare da sakin mutanen da ake garkuwa da su, da kuma tsagaita wuta a Lebanon “da za ta bai wa mutane damar komawa gidajensu cikin salama a dukkan ɓangarorin Blue Line.”
Ƙarin labarai 👇
2300 GMT –– An sace kayan abinci daga cikin motocin agaji kusan 100 a Gaza: MDD
An sace abincin da ke cikin motoci kusan 100 da ke ɗauke da kayan agaji da za a kai wa Falasɗinawa ranar 16 ga watan Nuwamba a wani mataki da ake gani yana cikin sata mafi muni a watanni 13 da aka kwashe ana yaƙi a yankin, inda yunwa take ƙara ƙamari, kamar yadda hukumomi biyu na MDD suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin.
Isra'ila ce ta umarci tawagar da ke ɗauke da kayan abincin ta hukumar UNRWA da Shirin Samar da Abinci na MDD su fice daga yankin ba tare da ɓata lokaci ba, sannan ta tilasta musu bi ta hanyar da ba a saba bi ba, wato hanyar Karem Abu Salem, a cewar Louise Wateridge, wata babbar jami'a ta UNRWA.
Ta ƙara da cewa an sace kayan abinci daga cikin motoci casa'in da takwas cikin motoci 109 da ke tawagar kuma an jikkata wasu daga cikin direbobinsu, ko da yake ba ta yi ƙarin bayani kan waɗanda suka kai musu harin ba.
"Wannan lamari ya nuna girman ƙalubalen da muke fuskanta wajen kai agaji a kudanci da tsakiyar Gaza," kamar yadda ta shaida wa Reuters.