Kotun Hukunta Manyan Laifuka t Duniya ICC da ke Hague ta ba da umarnin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant.
"Kotun ta ba da umarnin kamen mutanen biyu Mr Benjamin Netanyahu da Mr Yoav Gallant ne kan aikata munanan laifuka da laifuakn yaƙi a kan bil'adama aƙalla tun daga 8 ga watan Oktoban 2023 har zuwa aƙalla 20 ga watan Mayun 2024, wato ranar da Mai Shigar da Ƙara ya shigar da ƙorafin neman a kama su," in ji sanarwar.
ICC ta ce ba a bukatar amincewar Isra'ila a kan hurumin kotun.
A ranar 20 ga watan Mayu, Mai Shigar da Kara na ICC Karim Khan ya ce ya fitar da takardar sammaci ta kama Netanyahu da Gallanta saboda laifukan zaluntar bil'adama da aikata laifukan yaƙi a Gaza.
Netanyahu da sauran shugabannin Isra'ila sun yi tur da buƙatar Babban Mai Shigar da Kara na ICC Karim Khan ta kama su, suna mai cewa abin kunya ne kuma nuna wariya.
Shugaban Amurka Joe Biden shi ma ya caccaki Mai Shigar da Karar tare da bayyana goyon bayansa ga damar da Isra'ila take da ita ta kare kanta daga Hamas.
Sannan ICC ta buƙaci a kama shugaban Hamas Mohammed Diab Ibrahim al-Masri.