Amurka ta sha yin kira ga China, wadda ake gani a matsayin babbar mai adawa da ita a duniya, da ta ɗauki ƙarin matakai wajen shawo kan rikicin Gabas ta Tsakiya, ciki har da matsa lamba kan Iran. . / Hoto: AP Archive

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga takwarorinsa na China, Turkiyya, da sauran ƙasashe su "hana Iran mayar da martani" bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Damascus

Blinken ya yi magana ta wayar tarho da takwarorinsa na China, Turkiyya, Saudiyya, da Tarayyar Turai inda ya "bayyana musu ƙarara cewa bai kamata a ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya ba sannan ya buƙace su da su yi kira ga Iran kada ta mayar da martani," a kamar yadda kakakin Ma'aikatar Wajen Amurka Matthew Miller ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.

Kazalika Blinken ya yi magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant "domin jaddada goyon bayanmu mai ƙarfi ga Isra'ila kan duk wata barazana da za ta fuskanta," in ji Miller.

Iran ta sha alwashin mayar da martani bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta a Damascus ranar 1 ga watan Afrilun, inda ta kashe zaratan sojoji bakwai na runduna ta musamman ta Revolutionary Guards, cikinsu har da janar-janar guda biyu.

Amurka ta dakatar da ƴan ƙasarta daga tafiye-tafiye a cikin Isra'ila

Shugaban Amurka Joe Biden ranar Laraba ya ce ƙasarsa za ta bai wa Isra'ila "kariya mai ƙarfi", duk da sukar da yake yi wa Firaiminista Benjamin Netanyahu kan yaƙin da yake yi a Gaza.

Ranar Alhamis, Amurka ta taƙaita wa ma'aikata ƴan ƙasarta da iyalansu tafiye-tafiye zuwa wajen birnin Tel Aviv, da Yammacin Birnin Ƙudus da Be'er Sheva [Bir al-Sab da Larabci] "a matsayin wani kandagarki."

Amurka ta sha yin kira ga China, wadda ake gani a matsayin babbar mai adawa da ita a duniya, da ta ɗauki ƙarin matakai wajen shawo kan rikicin Gabas ta Tsakiya, ciki har da matsa lamba kan Iran.

Sai dai mahukuntan Beijing suna caccakar Amurka kan goyon bayan Isra'ila.

TRT World