Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar cewa kungiyar BRICS ta kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin hanzari za ta kara mambobi shida.
Ramaphosa ne ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wurin turonsu ranar Alhamis a Johannesburg.
"Mun yanke shawarar shigar da Jamhuriyar Argentina, Jamhuriyar Larabawa ta Masar, Jamhuriyar Tarayya ta Dimokuradiyyar Habasha, Jamhuriyar Musulunci ta Ira, Daular Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa cikinmu domin zama cikakkun mambobin BRICS,” in ji shi.
Ya kara da cewa wannan mataki zai soma aiki ne daga watan Janairu na shekarar 2024.
Labari mai alaka: BRICS na neman kalubalantar kasashen Yamma yayin da take fara taronta
Da ma dai kiraye-kirayen da aka rika yi na fadada kungiyar ta BRICS mai kunshe da kasashen Brazil, Russia, India, China da Afirka ta Kudu -- su ne suka mamaye ajandar taron na kwana uku.
Sai dai kungiyar, wadda ke daukar matakin bai-daya, ta amince game da "tsari da sharuda na fadada BRICS", in ji Ramaphosa.
Kasashe fiye da ashirin ne suka nemi shiga kungiyar, wadda take tafiyar da kashi daya cikin hudu na tattalin arzikin duniya kuma tana kunshe da mutane sama da biliyan uku.