The expedition crew had to battle adverse conditions to complete their 14,000-kilometer journey. / Photo: AA

Jami'an kimiyya na Turkiyya sun kammala Balaguron Kimiyya na Kasa a Yankn Antatika, inda suka dawo gida da bayanai masu muhimmanci da ke ƙarin haske kan sirrin da ke ɓoye a kudancin duniya.

Tawagar ta masu bincike Turkawa 24 sun dawo ƙasarsu a ranar Larabar nan bayan tafiyar kwanaki 36 mai cike da kalubale.

Kyaftin Dogac Baybars Isiler, mataimakin shugaban tawagar mai kula da kayayyakin amfani, ya bayyana cewa tawagar ta ci karo da manyan tuddan ƙanƙara a yayin tafiyar - wanda alamu ne na hatsarin sauyin yanayi da duniya za ta fuskanta.

Isiler ya kuma jaddada muhimmancin daukar matakan kariya a yayin da ake tafiya.

Ya ce "Yawaitar tuddan ƙanƙara a teku na nuni da tsagwaron hatsarin da ake fuskanta da dare da rana. Domin rage karfin wannan hatsari, ana yin tafiyar da duba hanya tare da amfani da injina masu wuta da na hangen nesa.

Ya kara da cewa "Sanya idanu da daukar matakan kariya yayin neman hanya don kar a ci karo da kankarar teku ko tuddan ƙanƙara na da muhimmanci wajen bayar da kariya ga jirgin ruwa, don tabbatar da an kammala zagayen ba tare da wata matsala ba."

A yayin wannan balaguro na binciken ilimi, tawagar Turkawan ta gudanar a bincike a bangarori daban-dabanda suka hada da nazarin muhalli da gurbatarsa da nazarin teku da ruwa da duniya da sararin samaniya da ƙasa da yanayin ƙasar da tsarin makamashi da auna duniyoyi da cigaba a fannin fitar da taswira.

Tafiyar kilomita 14,000

Bayan kammala ayyukansu a tsibirin Horseshoe, inda sansanin binciken kimiyya na Turkiyya yake, tawagar masu binciken ta ziyarci tsibirin Dismal, sanna ta tsallaka zuwa hanyoyin Lemarie da Doumer don isa ga tsibirin yaudara.

A nan sun hadu da masanan kimiyya na Spaniya su biyu da ke cikin jirgin ruwan TAE-VIII.

Bayan sun isa ga Tsibirin Livingstone, bayan zagayen awanni hudu, wani masanin kimiyyar Turkiyya d ake aiki a sansanin St. Kliment Ohridski mallakin Bulgaria, ya zo jirgin ruwan nasu.

Tawagar ta kimiyya, wadda ta kai kayan aiki a saninsanin kimiyya na Juan Carlos I mallakain Spaniya a wannan tsibiri, sun wuce zuwa Maldonado mallakin Ecuador a Tsibirin Greenwhich.

A wannan waje, wani masanin kimiyya dan Turkiyya da ke aiki da tashar ya je wajen tawagar. Daga baya tawagar ta is aga Tsibirin King George, wajen da za su je na karshe kafin Punta Arenas, bayan tafiyar awanni shida a tsakiyar iska mai karfi ta teku.

Bayan sun hau jirgin sama daga Tsbirin KIng George, ana sa ran za su dawo Turkiyya ta birnin Santiago na Chile Punta Arenas da Sao Paulo na Barazil.

Sakamakon rashin kyawun yanayi, dole ya sanya tawagar jira a jiirgin ruwa mai dauke da tutar Chile tsawon wata guda saboda an hana jiragen sama tashi da sauka.

A yayin da suke jira, masanan sun yi aiki kan bincikensu tare da karanta litattafai da yin tattaunawa.

A filin tashi da saukar jiragen sama na Teniente Rodolfo Marsh Martin da ke Tsibirin King George, da aka samarwa da hanyoyin tashin jirage inda a kullum ake yin zirga-zirga, an kasa ayyuka na tsawon kwanaki saboda yawaitar hazo.

A yayin da aka dawo da safarar jiragen sama, tawagar binciken sun ci gaba da tafiya zuwa Chile Punta Arenas zuwa Santiago, sannan zuwa Sao Paulo a Barazil. Sun kammala tafiyarsu ta kilomita 14,000 a Turkiyya.

TRT World