Gidauniyar Maarif na da makarantu 500 a kasashe 500. Hoto/Maarif Foundation

Daya daga cikin matakan da Turkiyya ta dauka bayan yunkurin juyin mulkin da kungiyar ‘yan ta’adda ta FETO ta yi a ranar 15 ga watan Yulin 2016, shi ne cika burin miliyoyin yara daga Afirka wadanda kungiyar ta so amfani da su domin yada farfagandarta.

FETO ta gina makarantu da ta rika tafiyarwa a matsayin wani bangare na ta'addancinta tun a shekarun 1990, har lokacin da ta kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya. Hakan ya sa kasar ta fito da wani tsari na sake inganta ilimin yara a fadin nahiyar.

Domin amsa kiran Shugaba Recep Tayyip Erdogan, da irin yarjejeniyar da ke tsakaninta da kasashen Afirka, gidauniyar Maarif, wadda ba ta neman riba, ta kwace makarantu 118 a 2016 wadanda a baya kungiyar ta FETO take jagoranta a kasashe 16 na nahiyar.

Yaran wadanda ake bukatar ceto su daga tsarin FETO na ta’addanci sun fara karatu ne tun daga ajin naziri har sakandire. An samu wannan ci-gaba ne ta hanyar goyon bayan da aka samu na kasashen Afirka.

Gidauniyar ta Maarif tana bai wa yara damar kara inganta kansu. Hoto/Maarif Foundation

Shekara bakwai kenan tun bayan da gwamnatin Turkiyya ta fito da wannan tsarin wanda yake bai wa miliyoyin yara daga Afrika damar ci gaba da karatunsu ba tare da FETO tana juya musu tunani ba, inda Gidauniyar Maarif ta kasance wata hanya mai karfi ta kyautata dangantaka tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka.

Ta hanyar amfani da doka ta musamman wadda Majalisar Dokokin Turkiyya ta yi, Gidauniyar Maarif – wadda aka samu sunanta daga kalmar Turkanci ta Daular Usmaniyya, na nufin ilimi ko kuma kalmar Larabci mai nufin hikima – inda aka kafa Gidauniyar a ranar 17 ga watan Yunin 2016.

Amincewar gwamnati

A tsawon shekarun da suka gabata, Maarif ta zama wani ginshiki na ci-gaba ta hanyar ilimi a Afirka, inda take amfani da kwararru don samar da tsarin karatu mai kyau da kuma bayar da horo wanda ya yi daidai da abubuwan da kowace kasa da ta ci gaba ke yi.

Sai dai wani babban bambanci da gidauniyar take da shi da kungiyar ta’addanci ta FETO shi ne bai wa daliban damar samun ilimi a darussa da suka hada da kimiyya da lissafi da ilimin zamantakewa tare da horar da su yadda ya dace domin fuskantar duk wani kalubale a nan gaba ba tare da saka musu wata akida ta siyasa ba.

A 2016, Gidauniyar Maarif ta kwace iko da sama da makarantu 118 wadanda a baya kungiyar ta'addanci ta FETO ke gudanarwa. Hoto/Maarif Foundation

Somalia ita ce kasa ta farko da ta soma mika makarantu bakwai ga Maarif wadanda a baya suke karkashin kungiyar FETO, abin da ke nuna amincin gwamnatin da gidauniyar.

A Tanzania, Maarif ta samu karbuwa sakamakon irin tallafin da take bai wa bangaren ilimi ta hanyar gudanar da sama da makarantu goma da ke da dalibai kusan 2,000.

Makarantun Maarif sun rinka haskakawa sakamakon wani tsari na musamman da suke da shi na mayar da hankali kan al’adun Afirka daga ciki har da harsunan Afirka da na Turkawa.

Duk shekara, sama da yara 1,000 daga Afirka na zuwa Turkiyya domin karatun gaba da sakandire ta hanyar tallafin gwamnatin Turkiyya.

Alaka da al’adu

Maarif ta yi fice wajen fitar da tsarin karatu mai kyau da kuma bayar da horon da ya dace da ya zo daidai da irin bukatun kowace kasa na samun ilimi mai kyau kan kimiyya da lissafi da zamantakewar dan adam, don su zama cikin shirin yaki da duk wasu munanan akidu da ake da su a duniya a yau.

Somalia ta kasance kasa ta farko da ta mika wa Maarif sama da makarantu bakwai mallakar FETO. Hoto/Maarif Foundation

Domin samar da dalibai masu ilimi, gidauniyar ta Maarif ta ci gaba da kokarin da take yi a makarantu 447 da ke kasashe 51 inda kuma take gudanar da makarantun koyar da sana’o’i.

Sama da dalibai 500,000 daga duka kasashen na samun horo na musamman a makarantun boko da na gargajiya, da kuma koyon sana’o’i daga Gidauniyar Maarif wadda ke da makarantu 500 a kasashe 51.

Gidauniyar ta Maarfi ta samu daukaka a Tanzania kan irin tallafin da ta bayar ga bangaren ilimi wanda ya hada da kula da sama da makarantu 10 da ke da sama da dalibai 2,000.

Gidauniyar ta soma koyar da al’adun Turkiyya da na Afirka da sauran harsunan kasashen duniya da Turkanci.

Gidauniyar tana kuma mayar da hankali wurin koyar da dalibai a Afirka al'adunsu da kuma na Turkiyya. Hoto/Maarif Foundation

Gidauniyar Maarif ta taimaka matuka wurin habaka ilimin yara da kuma baiwarsu ta hanyar tallafa wa karatun yara daga kasashe masu tasowa a kyauta inda take hada gwiwa da ma’aikatun ilimi a kasashen.

Haka kuma gidauniyar na bai wa matasa da ke da baiwa damar kara inganta kansu. Ta wannan bangaren, gidauniyar ta Maarif na da burin fadada tsarin ilimi ga duniya baki daya.

Wannan na jawo gidauniyar ta Maarif kusa da tsarin da take da shi na kin neman riba da kuma budadden tsari ba kamar makarantun FETO da ke aiki ta karkashin kasa ba a fadin duniya.

Turkiyya ta bayar da gudunmawa ta bangaren karatun gaba da sakandire a duniya baki daya wanda ba za a iya kawar da ido daga kai ba a shekaru bakwai da suka gabata.

Shugaban Gidauniyar Farfesa Birol Akgun ya ce alaka tsakanin Afirka da Turkiyya ta hanyar ilimi abu ne na tinkaho. Hoto/Maarif Foundation

Shugaban Maarif, Farfesa Birol Akgun, ya bayyana cewa Gidauniyar na tallafawa wurin alakanta al’adu Turkiyya da Afirka.

Karramawa babba

Domin magance matsalolin da kasashen Afirka ke fama da su da kuma tallafa wa tattalin arzikinsu, da sojoji da siyasarsu da Turkiyya, ya bayyana cewa gidauniyar na son biyan bukatun mutanen nahiyar.

“Muna aiki tukuru domin kulla dangantaka. Girman ci gaban masana'antu da samun ilimi a Turkiyya ya zama abin koyi ga ƙasashen Afirka.

A Togo, Gidauniyar Maarif ta kafa dandalin wasanni, da zummar samar da wata alaka tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na kasar da takwarorinsu na Turkiyya da kwalejojin wasanni da jami’o’i da tsangayoyin kimiyyar wasanni da musayar kwarewa, da taimako a aikace da tsara ayyukan wasanni daban-daban don haɓaka haɗin gwiwa.

“Muna kokari sosai domin zama cikin wannan dangantaka. Ababen more rayuwa na Turkiyya wani abin kwaikwayo ne ga kasashen Afirka kan irin matakin da ta kai a bangaren ci gaban masana’antu da ilimi," in ji Farfesa Birol Akgun.

Makarantun Maarif sun kuma samu yabo iri-iri. Maarif ta samu karramawa mai girma daga Ma’aikatar Ilimi ta Djibouti kan ilimi tsakanin 2018-2019.

A gasar kungiyoyi 73 ta hada mutum-mutumi ta 2019 ta Lego Arabia wadda aka yi a Jordan, daliban Tunisia daga makarantar Maarif sun samu karramawa ta musamman daga alkalan gasar.

Tsarin tallafin karatu ta kungiyar ya taimaka wa sama da dalibai 15,000. Hoto/Maarif Foundation

A Disambar 2022, wanda ya zo na farko a shirin darasin ilimin halitta mai taken “kwatanta tsarin ruwa da ci gaban kasa” ya fito ne daga makarantar Maarif ta Turkiyya da ke Zanzibar.

Maheen Masoud, wanda dalibi ne daga makarantar Pak-Turk Maarif School da ke gundumar Lahore ta Pakistan shi ya zo na daya, a gasar makarantun sakandire ta lissafi a Yunin 2021.

Tasirin tallafin karatu

Bugu da kari, makarantun Maarif da ke a Nijar sun zo na farko a bangaren kiwon lafiya da tsaftar muhalli inda suka sha gaban makarantu da dama. Maarif na hada gwiwa da jami’o’in Turkiyya domin bai wa dalibai karin ilimi.

Har zuwa wannan gabar, cibiyoyi a Turkiyya sun yaye kusan dalibai dubu goma daga Afirka.

Tsarin tallafin karatun ya taimaka wa sama da dalibai 15,000. Wannan adadin ya nuna yadda ake samun karuwa ta bangaren kusancin da ake samu tsakanin Turkiyya da Afirka a kullum.

"Za mu karfafa dankon zumunci da 'yan uwantaka da gaskiya da kasashen Afirka." Shugaba Erdogan ne ya yi wannan jawabin a birnin Santambul kan batun hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka a 2021.

“Da gaske ne nasarorin da aka samu na Ilimin Turkiyya ta hanyar makarantun Maarif tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Turkiyya sun zama dalilai ne na alfahari da kuma taimakawa don kara inganta dangantaka da kyakkyawar makoma tsakanin Afirka da Turkiyya," in ji Farfesa Birol Akgun.

TRT Afrika