'Yan ta'addan FETO na ci gaba da samun mafaka a Amurka da Jamus, shekara bakwai bayan yunkurin juyin mulki

'Yan ta'addan FETO na ci gaba da samun mafaka a Amurka da Jamus, shekara bakwai bayan yunkurin juyin mulki

Duk da kiraye-kirayen da Ankara ta sha yi, har yanzu Amurka da Jamus ba su dauki muhimman mataki na dawo da shugaban FETO ko mambobin kungiyar Turkiyya ba.
Shekara 7 kenan bayan al'ummar Turkiyya sun kare dimokuradiyyarsu daga masu yunkurin juyin mulki. / Hoto: AA Archive

A wata tattaunawa da aka yi a wannan makon don juyayin ranar 15 ga watan Yuli, lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasaba ba a Turkiyya, Daraktan Sadarwa na kasar Fahrettin Altun ya yi kira na musamman ga kasashen duniya su hada kai domin yakar kungiyar 'yan ta'adda ta FETO.

Shugabannin FETO ne suka jagoranci yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji marasa kishi suka yi a wani dare a 2016, abin da ya yi sanadin mutuwar fararen-hula sama da 250 sannan dubbai suka jikkata.

“FETO kungiyar 'yan ta'adda ce ta duniya, kuma kamar yadda ake yaki da sauran kungiyoyin ta'addanci, ya kamata duniya ta hada kai domin yakar ta,” a cewar Altun a wani sakon bidiyo da ya fitar, yana mai tuna wa duniya cewa masu ikirarin kasancewa “abokan” Turkiyya sun yi gum da bakunansu lokacin da al'ummar kasar suke kare dimokuradiyyarsu.

Altun ya bayyana dalilansa na yin wannan kira.

Tun lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin, Turkiyya ita kadai ce take wannan yaki da 'yan ta'adda, ciki har da bin hanyoyin diflomasiyya don ganin an dawo mata da mutanen da suka kitsa wannan danyen aiki gida daga kasashen da suke samu mafaka.

Amurka da Jamus su ne kan gaba wajen bai wa 'yan ta'addan FETO mafaka, ciki har da shugaban kungiyar Fetullah Gulen.

Ko da yake an bayar da gamsassun shaidu domin soma yi masa shari'a, amma Amurka ba ta dauki wani mataki da ya dace ba domin bincikarsa da ma harkokin kasuwancinsa.

TRT World ta yi nazari kan mutanen da Ankara ta fi nema ruwa-a-jallo a duniya da kasashen da suka fi ba su mafaka:

Amurka ta zama maboya

Amurka ta kasance mafaka ga mambobin FETO da dama, wadanda akasarinsu suka tsere daga Turkiyya, bayan sun gaza kwace kasar da karfin soja.

Fetullah Gulen shi ne kan gaba da aka fi nemi a cikin mambobin FETO kuma tun 1999 yake zaune a Amurka.

Cevdet Turkyolu, daya daga cikin manyan na hannun-daman Gulen kuma mai harkokin sayar da gidaje, yana cikin manyan mambobin FETO da suke zaune a Amurka.

Turkyolu, wanda yake zaune Saylorsburg da ke jihar Pennsylvania, kuma shi ne yake shirya wa Gulen taruka a matsayin “sakatarensa” a wurin shakatawa na Golden Generation Chestnut Camp Retreat, wata cibiya da ke zagaye da bishiyoyi.

Turkiyya ta yi amannar cewa Turkyolu ne yake kula da harkokin kudin kungiyar, kuma yana karbar umarnin Gulen don sanya miliyoyin dala daga cikinsu a harkokin kasuwanci.

Aydogan Vatandas, yana daya daga cikin manyan masu watsa farfagandar FETO kuma shi ne yaker kula da shafin Twitter mai suna 'Fuat Avni’, inda ake kallonsa a matsayin ‘danlelen’ Fetullah Gulen.

Vatandas, wanda ake bincika bisa jagorantar kungiyar 'yan ta'adda a Istanbul, an bayar da rahoton cewa yana cikin masu gudanar da shafin Twitter na Fuat Avni Twitter, wanda ake amfani da shi wajen watsa labarai da FETO ta samu ta hanyar leken asirin jama'a ta wayar tarho kafin da kuma bayan yunkurin juyin mulki.

Lokacin da Vatandas ya tabbatar an gano shi, ya zille wa masu bibiyarsa tare da samun taimakon masu leken asiri na FETO inda ya gudu zuwa Amurka bayan ya bi ta Jamus.

Emre Uslu, wani mai laifi da rundunar 'yan sandan duniya take nema ruwa-a-jallo, an yi amannar yana zaune a Amurka.

Bayan ya tsere daga Turkiyya, yanzu yana zaune a wani gidan kasaita a Fairfax da ke jihar Virginia, wanda aka ce shi ne ya saya.

Tuncay Opcin, shi ma wani mai laifi ne na FETO da yake zaune a Amurka, kuma yana cikin masu yi mata leken asiri da suka taimaka wajen yin kutse a rundunar sojin Turkiyya (TSK).

Munafuncin Jamus

Lamari ne da ke a bayyane kan cewa wasu sanannun mutane na kungiyar FETO, daga ciki har da wadanda Turkiyya ke matukar nema kan zargin ta’addanci Abdullah Aymaz da Mehmet Ali Sengul, sun samu mafaka a Jamus.

Aymas, wanda ya soma alaka da FETO a lokacin da jagoranta Fetullah Gulen bai yi fice sosai ba a Izmir, na da mukami a cikin kungiyar ta Gulen.

Ana danganta Aymaz da wani ‘Limamin Turai’ na kungiyar Feto wanda kuma jagora ne wanda yake da alhakin kula da mabiyan kungiyar da dama a yankin.

Watanni kadan kafin yunkurin juyin mulkin na 2016, Aymaz ya rubuta wata makala a wata jarida mai alaka da Feto, wadda ya alamta yiwuwar juyin mulkin.

Ya bar Turkiyya daf da yunkurin juyin mulkin da aka dakile. Wani kuma babba da ke cikin kungiyar ta ta’addancin, Mehmet Ali Sengul an bayar da rahoton cewa shi ne ake ganin zai gaji Gulen, kuma yana zaune a Jamus.

Haka kuma wani mutum wanda ke da alaka da FETO da kuma yunkurin juyin mulkin na 2016, wanda ake ganin yana boye a Jamus, shi ne Adil Oksuz.

Ana zargin Oksuz ne ma ya kitsa yunkurin na juyin mulkin.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya bayar da rahoton cewa Oksuz yana zaman wucin gadi a Berlin bayan yunkurin juyin mulkin.

Zekeriya Oz, Fikret Secen, Celal Secen da Ilham Polat na daga cikin wasu mambobin kungiyar ta’addancin da ke zaune a kasar ta Jamus.

A matsayinsu na ‘yan kungiyar FETO wadanda suka nemi mafaka a wadannan kasashen na Yamma, ana nuna damuwa kan karancin matakin da kasashe kamar Amurka da Jamus suka ki dauka domin tasa keyar mutanen da kuma girbar abin da suka shuka kan hannunsu a yunkruin juyin mulkin.

Har yanzu ba a amsa kiraye-kirayen gwamnatin Turkiyya da ta ya sha yi ba neman hadin kan kasashe domin yaki da kungiyar FETO da kuma kungiyoyin ta’addanci da ke alaka da ita.

TRT World