Turkiyya za ta ci gaba da yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka hada da PKK da Daesh da Kungiyar Ta’addanci ta Fethullah (FETO), in ji daraktan sadarwa na kasar Fahrettin Altun.
A yayin Taron Babbar Manufar Turkiyya da aka gudanar a Ankara, Altun ya bayyana yadda Turkiyya ta fuskanci kalubale ga tsaro da zaman lafiya da dimokuradiyyarta.
Ya kara da cewa “A lokacin da muka kakkabe barazanar ta’addanci ga kasarmu a ciki da wajenta, muna kuma ci gaba da yakar kungiyoyin ta’adda kamar su PKK da reshenta na Siriya PYD/YPG, Daesh da FETO… Turkiyya ba za ta taba bayar da kai bori ya hau ba game da yaki da ta’addanci.”
Altun ya ci gaba da cewa a lokacin da Turkiyya ke tabbatar da tsaron kasarta, tana kuma bayar da gudunmawa ga tsaron yankunanta da ma duniya baki daya, "saboda yadda take yaki da ta’addanci."
Turjiya ta bai daya
Da yake tsokaci kan Turkiyya ba za ta ja da baya ba kan ayyukan kalubalantar duk wasu matsaloli, Altun ya ce “Mun nuna yadda muke kwantar da hankali da kawar da rikice-rikice, musamman ma a rikicin Rasha da Yukren.”
Ya ce “A matsayinmu na kasashen da ke magana da yaren Turkanci, mun fahimci hadin kan da ke tsakaninmu ba yana kara mana karfi ba ne kawai, yana kuma ba mu gudunmowar kalubalantar duk wasu matsaloli da kalubale da ke tunkaro mu a yankunanmu da ma duniya baki daya.”
Darkatnan Sadarwa na Turkiyya Altun ya kara da cewa “Tare za mu ciyar da kawunanmu da al’adu da dabi’unmu gaba, wadanda suke bayyana ko mu su waye.”