Kusan mutane 250 aka kashe yayin da aka jikkata sama da 2,000 a yayin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Hoto: AA

An kai hare-hare ta sama kan ginin majalisar dokoki a babban birnin Ankara inda sojoji suka kutsa kai hedikwatar jami’yyar AK sannan suka yi garkuwa da Shugaban Rundunar Sojin Turkiyya Hulusi Akar.

A lokacin da ake ta jin karar harba bindigogi da fashewar bama-bamai a Ankara da Istanbul, ‘yan kasar sun fita kan tituna don kalubalantar juyin mulkin – inda wasun su suka dinga tunkarar tankokin yaki da motocin igwa.

Hakan ya yi sanadin mutuwar akalla 250 da jikkatar sama da mutum 2,000.

Mahukunta sun bayyana Fethullah Gulen da kungiyarsa ta ta’adda ta FETO a matsayin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin.

Dubban mutanen da aka zarga da wannan aika-aika sun tsere daga Turkiyya, awanni bayan juyin mulkin, da yawan su suna zaune a kasashen Turai.

Shiri na tsawon shekaru

Mahukuntan Turkiyya sun bayyana cewa FETO ta dauki tsawon lokaci tana gudanar da ayyuka a kasar.

Kafin yunkurin juyin mulkin, kungiyar ta yi kokarin samun iko kan yanayin siyasar Turkiyya ta hanyar shiga da kutsa kai cikin dukkan hukumomin gwamnati.

Fethullah Gulen, wanda yake jagorantar gungun ‘yan ta’addar, yanzu haka yana samun kariya daga Amurka a birnin Pennsylvania. Ana zargin sa da yin shiri na tsawon lokaci don kifar da gwamnatin Turkiyya.

Gulen ya fara harkokinsa a 1960 a matsayin malamin addini don zama mai fada a ji a siyasar Turkiyya, kuma ya yi ayyukan kafa kungiyar da za ta yadu a dukkan sassan duniya.

Masu sharhi sun ce ya yi hakan ne ta hanyar bude makarantu da suka rika ayyukan leken asiri a kasashen waje – daga Amurka zuwa tsakiyar Asiya, Afirka da Turai.

Amma tun bayan rashin nasarar yunkurin juyin mulkin 15 ga Yuli a Turkiyya, karfin kungiyar ya yi rauni sosai a kasashe da dama inda mutane suke nesanta kawunansu da ita.

“Alal misali, a makarantunsu, a baya za ka samu dalibai da malamai da yawa ‘yan kasar Turkiyya, amma bayan abin da ya faru a 2016 sai lamarin ya canja. Kazalika a asibitocinsu wannan adadi ya ragu sosai,” a cewar Kabiru Adamu, shugaban kamfanin bayar da shawarwarin tsaro na Beacon Consulting a Yammacin Afirka, a hirar da ya yi da TRT Afirka.

Kakkabe ayyukan kungiyar

Makarantun FETO sun yi kaurin suna wajen zama wuraren daukar sabon jini da za su dinga gudanar da munanan ayyukansu.

Da fari ana fake wa da sunan yi wa addini hidima, ana wa’azi da tattaunawa, sannan sai dinga saka mambobinsu a cikin soji da ‘yan sanda.

Wasu ‘yan kasuwarsu da farfesoshi da ke koyarwa a jami’a na daga cikin wadanda aka zarga da aiki tare da kungiyar ta ta’adda.

Wata hanya ce ta yin cuwa-cuwa wajen daukar aiki, inda suke mayar da daliban da suka kammala digiri a matsayin ma’aikata da ake sauyawa tunani.

Bayan yunkurin juyin mulkin, baki ya zo daya tsakanin gwamnati da ‘yan adawar Turkiyya kan a yi maganin kungiyar nan take.

Gwamnati ta yi ta rufe wa da kwace matsugunan FETO a cikin Turkiyya, inda take kuma ci gaba da jan ra’ayin kasashen duniya don korar su daga daga kasashensu.

A Turkiyya, an kori mambobin kungiyar ta’adda ta Gulen daga ayyukan gwamnati, musamman ma a soji da sauran hukumomin tsaro.

An kakkabe dukkan mutane da cibiyoyi da aka gano suna da alaka da kungiyar ta FETO.

Kazalika gwamnati ta rufe cibiyoyin ilimi sama da 1,000 da suke karkashin FETO a Turkiyya, inda kasar ta yi kira ga kawayenta da su dauki irin wannan mataki.

Jami’an tsaron Turkiyya sun kama mambobin FETO da dama a farmakin da suka kai a kasashen waje tare da dawo da su Turkiyya don gurfana a gaban shari’a.

Misali a 2021, an kama Salahaddin Gulen, dan uwan shugaban FETO a Kenya a wani farmaki da Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya ta gudanar. Ana zargin sa da zama mamban kungiyar ta’adda ta FETO.

Tsawon shekaru, Turkiyya ta yi ta kokarin ganin an dawo mata da Fethullah Gulen daga Amurka. Turkiyya ta kuma bukaci a dawo mata da mambobin kungiyar daga kasashen duniya 27.

FETO a Afirka

‘Yan ta’addar FETO na gudanar da kungiyar a dukkan fadin duniya. A yayin da aka kassara wadanda suke Turkiyya, akwai wasu daruruwan makarantun kungiyar da ke ci gaba da ayyuka a kasashen Afirka.

Ana yi wa makarantun kallon masu samar da kudin-shiga ga kungiyar.

Mahukuntan Turkiyya sun samu nasarar roka da jan ra’ayin wasu gwamnatocin Afirka don daukar matakan rufe makarantun FETO a kasashensu.

An ga hakan Sudan, Guinea, Mali, Somalia, Muritania, Nijar, Chadi, Tunisia da Senegal.

Matakin na Turkiyya ya sanya an rufe makarantun ko mika wa Gidauniyar Maarif ta Turkiyya su. Gidauniyar ce da Turkiyya ta samar don gudanar da ayyukan ilimi a kasashen duniya, da kuma karbe makarantun da ke karkashin FETO tare da ci gaba da kula da su, da ma bayar da tallafin karatu.

Amma kuma duk da haka, Turkiyya na fuskantar kalubale wajen jan ra’ayin wasu kasashen Afirka kan su dakatar da ayyukan FETO da kasuwanci da suke yi a kasashensu.

Wasu masu nazari na cewa FETO na boye manufarta a wuraren da take ayyuka.

“Wasun su sun canja mallakin makarantun, wasu sun sauya musu sunaye da siffofi don bad-da-kama. Yana da wahala farat-daya a gano kudiri da manufar da ke cikin zuciyar FETO,” in ji Mallam Kabiru Adamu, wani masani kan harkokin tsaro a Nijeriya.

Ya kara da cewa: "Duk da cewa har yanzu Turkiyya ba ta gama nasara kan FETO dari bisa dari a kasashen waje ba, ayyukan diflomasiyyata sun yi nasarar rage karfin kungiyar sosai a kasashen duniya.”

TRT Afrika