Ozturk ya shafe shekaru biyu da rabi yana gudanar da binciken a jami’ar Havard da ke ƙasar Amurka. Hoto: AA      

Daidai lokacin da yake kammala digirinsa na uku a fannin kimiyyar Fiziya (nazarin juyawar al’amura) a Jami’ar Havard, matashin Ba’Turken ya gano sabuwar mahangar fahimtar tushen asalin rayuwa a doron ƙasa, al’amarin da ya faranta wa masanan kimiyya rai.

Rukunin masu binciken da Furkan Ozturk ya gudanar, an wallafa sakamakon a Mujallar nazarin nau’ukan ci gaban da ya samu a fagen kimiyya ta. Sun ƙara samun ci gaba wajen fahimtar tushen rayuwa na bai-ɗaya.

Sun bijiro da cewa, akwai yiwuwar maganaɗisun ma’adanai da aka samu tun farkon duniya sun yi tasirin zaɓen ƙwayoyin halittar da suka siffantu da bayyana a mudubin juna akan sauran.

Cikin shekarar 1848, Bafaranshen Masanin kimiyyar sarrafa sinadarai Louis Pasteur ya ɓullo mahangar bai-ɗaya, al’amarin da ke nuni da wasu sinadarai da ya zama dole sai da su halittar madubin juna za ta wanzu, tamkar dai misalin hannayen hagu da dama.

Kodayake akwai buƙatar gudanar da ƙarin bincike don warware sirrin ɓoye ɗungurungum, boda haka masana kimiyya ke da tabbacin cewa, abin da Ozturk ya gano muhimmiyar matsaya ce, ta fahimtar muhimman al’amura ke juyawa wajen faruwar rayuwar.

‘Haƙiƙanin babbar mahangar fahimta.’

Wannan mahanga da aka gano ana sa ran za ta yi ƙarin haske game da tushen asalin rayuwa a doron ƙasa, tare da al’amuran rayuwa da suka wakana ta gefen ɓoye a doron duniya, inda ɗaukacin al’amuran ke kai-kawon tsarin juyin sinadarai na bai-ɗaya, kuma yake nuni da fifikon nau’ukan siffofin madubin juna da ke harhaɗo sinadaran ƙwayoyin halittu.

“Tabbas wannan ce, haƙiƙanin babbar mahangar fahimtar tsarin juyawar sinadarai na bai-ɗaya da ke da muhimmancin farar da rayuwa, sannan wannan yiwuwa ne, kuma tabbas akwai yiwuwar hakan- an warware matsala,” a cewar masanin kimiyyar haɗakar nazarin halitta-da-ta sarrafa sinadarai da ya samu lambar yabo ta Nobel, Jack Szostak, kamar yadda mujallar ta ruwaito.

Ozturk, wanda ya samu digirinsa na farko daga Jami’ar Bilkent da ke Ankara, babban birnin Turkiyya, ya shafe shekaru biyu da rabi yana bincike a Jami’ar Havard.

“Muna neman musabbabin haɗuwa ta zahiri da za ta karya lagon siffar madubin juna ta bai-ɗaya da ake iya bambancewa.

Bincikenmu ya bayyana maganaɗisun ma’adanai masu yawa da suka wanzu (aka same su), kuma ana ganin su ɗamfare da maganaɗisu, na iya sawa a kai ga gacin karya lagon tsarin na bai-ɗaya.

Gwaje-gwajen da muka gudanar sun nuna cewa sararin maganaɗisu ya haɗu da sinadaran ƙwayoyin, sannan maganaɗisun ya yi matuƙar tasirin tafiyar da wannan tsari na bai-ɗaya,” a cewarsa.

“Mun fara ganin ɓurɓushin rayuwa ta farko a doron duniya

‘Kimanin shekaru biliyan huɗu da suka wuce, wato kimanin shekaru miliyan 500 bayan haɗuwar dandazon duniyoyi da taurari da duniyarmu, sai muka fara ganin alamun rayuwa ta farko a doron duniya,” kamar yadda Masanin Fiziya ɗan shekara 26 ya bayyana wa Anadolu.

Dangane da tasirin abin da binciken ya gano, ya ce,”Bincikenmu wani haske ne game da tushen asalin rayuwa, wani rikitaccen al’amari a duniya.

Wannan tamkar warware matsalar, inda muke da taƙaitacciyar hujja daga shekaru biliyan huɗu (4) da suka wuce. Nazarinmu zai bayar da muhimmiyar gudunmuwar fahimtar tushen asalin rayuwa.

“Kodayake ba mu da tabbaci kan yadda ɗaukacin al’amura suka haɗu a bangare guda, wannan abin da binciken ya gano zai taimaka wajen amsa tambayoyin, tare da buɗe kafar fahimtar yadda rayuwa ta fara.

Fahimtar yadda rayuwar duniya ta fara ya ƙara bunƙasa iliminmu game da sharuɗɗan rayuwa a wani wuri daban. Wannan ilimin zai kasance jagora wajen binciken yadda rayuwa take a wani gefen fake, wanda ba doron wannan duniyar ba. Sai dai har yanzu samun tabbaci ne ƙalubalen, amma akwai yiwuwar hakan,” a cewarsa.

TRT World