Yunkurin juyin mulkin FETO a 2016: Mummunar ranar da ta sauya zuwa kulla alaka mai kyau tsakanin Turkiyya da Afirka

Yunkurin juyin mulkin FETO a 2016: Mummunar ranar da ta sauya zuwa kulla alaka mai kyau tsakanin Turkiyya da Afirka

Shekaru bakwai da suka gabata ne 'yan ta'adda na kungiyar FETO suka yi kokarin kifar da zababbiyar gwamnatin Turkiyya.
Shekaru bakwai bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba dimukradiyyar Turkiyya na ci gaba da habaka. Hoto: AA

Daga Ebubekir Yahya

A daren 15 ga Yulin 2016, wasu sojojin Turkiyya da suka yi tawaye da ke biyayya ga Kungiyar ‘Yan ta’adda ta Fetullah Terrorist Organization (FETO) sun yi yunkurin kifar da zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya a kasar.

Daren ya zama mafi muni a tarihin siyasar Turkiyya, dare ne mummuna da aka ci amanar kasa.

Babu wanda ya iya tsinkayar abin da ke faruwa a farkon lamarin.

‘Yan ta’adda da suka shiga inuwar rundunar soji, sun dinga luguden wuta kan fararen-hula da ya kamata a ce suna kare wa.

Jiragen yaki sun dinga shawagi suna ruwan bama-bamai kan fararen-hula na tsawon awanni, inda suka jefa kasar cikin halin dimuwa.

A tsawon dare daya tilo, cin amanar kasa da ‘yan ta’adda na FETO suka yi, ta yi sanadin shahadar mutum 249 a fadin Turkiyya, yayin da mutum 2,196 suka samu raunuka, mafi yawa a biranen Istanbul da Ankara.

An murkushe yunkurin juyin mulkin bayan Shugaba Erdogan ya yi kira ga jama'a su fita kan tituna don kare makoma da dimokuradiyyar Turkiyya. Hoto: AA

Al’amarin ya sauya da tsakar dare, a lokacin da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayip Erdogan ya yi kira ga ‘yan kasa ta gidan talabijin mai zaman kansa da amfani da intanet inda ya sanar da su abin da ke faruwa.

Shugaban ya yi kira ga jama’arsa da su hada kansu, su fita kan tituna su kalubalanci masu yunkurin juyin mulkin don kubutar da dimokuradiyya da makomar kasarsu.

A yayin da aka amsa kiran da Shugaba Erdogan tare da kalubalantar ‘yan ta’addar, gwamnati ta kakkabe mambobin FETO da ke ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Bayan shekaru bakwai, dimokuradiyyar Turkiyya na ci gaba da habaka, sannan makomar kasar ke ci gaba da yin kyawu.

An kassara masu yunkurin juyin mulkin awanni bayan an fafata da su. Hoto: AA

Jan hankali ga Afirka

Sakamakon yadda bijirewa da juriyar al’umma suka kawar da yunkurin juyin mulkin FETO bayan sun yi kaka-gida a rundunar soji, an samu sauyin manufa a manufofin Turkiyya a kasashen ketare, musamman ma yadda kasar ke mu’amala da kasashen Afirka.

‘Yan ta’addan FETO sun tsere kasashen waje da dama, musamman Amurka, kasar da shugaban ‘yan ta’addan Fethullah Gulen ke zaa a yanzu, tare da bai wa mabiyansa umarni sama da shekaru talatin.

Kasashen Afirka ma sun ga yadda ‘yan ta’addan FETO suka dinga tururuwar shiga cikinsu, suna haduwa da mambobinsu a wadannan yankunan da suke yin abubuwan da ke da alamun tambaya, musamman ma kafa makarantu.

Akalla mutum 249 a fadin Turkiyya ne suka yi shahada, sannan mutum 2,196  suka samu raunuka a daren. Hoto AA

A kokarin ganin an kassara kungiyar ta’adda ta FETO gaba daya tare da toshe duk wata hanya da take samun kudade, Turkiyya ta fara tuntubar kasashen Afirka, inda take gargadin su kan hatsarin da ke tattare da gungun ‘yan ta’addan a cikin iyakokinsu.

A lokuta daban-daban, Shugaba Erdogan ya ja hankalin shugabannin Afirka game da hatsarin da ke tattare da FETO a kasashensu, yana bayyana musu cewa ko ba jima ko ba dade, kungiyar za ta iya zama silar aukuwar abu makamancin wanda ya auku a daren 15 ga Yulin 2016 a Turkiyya.

Shugaba Erdogan ya karfafa alakar kasarsa da nahiyar Afirka. Hoto: AA

Ministan harkokin wajen Turkiyya na wancan lokacin Mevlut Cavusoglu ma ya gana da takwarorinsa da dama daga kasashen Afirka, inda ya dinga bayyana musu yadda FETO ta yi yunkurin kifar da gwamnatin dimokuradiyya a kasar.

Ya bayyana barazanar wannan kungiya a kasashen da mambobinta suka samun mafaka.

Mahukuntan Turkiyya sun bai wa kasashen Afirka shawarar kora ko mika musu ‘yan ta’addan FETO, sannan su mika makarantun da suke da gudanarwa ga Gidauniyar Maarif, wadda gwamnati ta kafa don amfanar jama’a.

Karfafar kawance da Afirka

Kokari da gwagwarmayar Turkiyya wajen karfafa alaka da hadin kai da nahiyar Afirka ya zama wani darasi ga ayyukan sauran kasashe wajen kyautata dangantaka ga kasashen waje.

Babban Taron hadin Gwiwar Afirka-Turkiyya da aka gudanar daga 17 zuwa 21 ga Disamba na 2021, ya samu halartar shugabannin Afirka da dama.

A jawabinsa a wajen taron, Shugaba Erdogan ya nemi goyon baya da hadin kan shugabannin Afirka, kuma ya jaddada cewa hadin kan zai amfani dukkan bangarorin biyu.

Hukumomin Turkiyya irin su TIKA, Yunus Emre da Gidauniyar Maarif sun gudanar da ayyuka da dama a Afirka a fannonin ilimi, lafiya da samar da kayan more rayuwa ba tare da tsammanin ramako ba.

Turkiyya na son karfafa kasuwanci da zuba jari a Afirka zuwa dala biliyan $75. Hoto: AA

Turkiyya ce kasa ta farko a duniya wajen bayar da taimako ga dan adam idan aka kwatanta da kudaden shigar da kasashe ke samu.

Kasashen Afirka sun ga yadda Turkiyya take kara zuba jari kai-tsaye a cikinsu, inda kamfanoninta da dama suka kafa rassansu a nahiyar Afirka.

Yawan jarin tsakanin Turkiyya da Afirka ya haura dala biliyan $30.

A lokacin da yake bayani ga mahalarta babban taron Tattalin Arziki na Turkiyya-Afirka karo na uku a Istanbul da aka yi a tsakanin 21 da 22 ga Oktoban 2021, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa “manufarmu ita ce mu kara yawan jari a Afirka zuwa dala biliyan $50, da kuma karin dala biliyan $75.”

Farfesa Yunus Turhan, Daraktan Cibiyar Ayyuka da Bincike Kan Tekunan Bahar Maliya da Tsangayar Afirka ta Jami’ar Hacı Bayram-ı Veli da ke Ankara yana ganin wannan alaka ta kasuwanci tana karfafa dangantaka tsakanin Turkiyya da Afirka.

An samu ziyartar juna mai amfanar kowanne bangare tsakanin shugabannin Turkiyya da na Afirka. Hoto: AA

Turhan ya shaida wa TRT Afirka cewa “A 2013, yawan jarin tsakanin Turkiyya da Afirka ya kai dala biliyan 21.5, a 2014 ya ragu zuwa dala biliyan 20.7, inda a 2015 kuma ya sake raguwa zuwa dala biliyan 18.

A 2016, jarin ya kasance dala biliyan 17, a 2018 kuma ya karu zuwa dala biliyan 22. A 2019 adadin ya karu zuwa dala biliyan 22.4, sai a 2020 da ya tashi zuwa dala biliyan 22.6. A 2022 kuma, jari tsakanin Turkiyya da nahiyar Afirka ya kama dala biliyan 33.”

A tsakanin 2016 da 2023, an gudanar da manyan tarukan kasuwanci da karawa juna sani da karfafa alakar Turkiyya da Afirka, sannan a sake daukaka alakar zuwa wani mataki na musamman, a lokacin da kasashen duniya ke gogayya a nahiyar.

A lokacin bude TRT Afirka a watan Maris na 2023, an gudanar da taron Sanin Makamar Aikin Kafafen Watsa Labarai na TRT-Afirka, wanda 'yan jarida daga kasashen Afirka daban-daban da mambobin Kungiyar Yada Labarai ta Afirka suka halarta.

Ana kallon kaddamar da Sashen TRT Afirka da ke yada shirye-shirye a intanet mai taken ‘Afirka tsantsarta’, a matsayin wata gaba mai muhimmanci a bunkasa alakar Turkiyya da Afirka. Sashen na gabatar da shirye-shirye a harsuna hudu; Ingilishi, Faransanci, Hausa da Swahili.

Kaddamar da TRT Afirka a watan Maris din 2023 ya zama wani babban mataki na bunkasa alakar Turkiyya da Afirka. Hoto: AA

Ziyarar Shugaban Kasa

Recep Tayyip Erdogan ne shugaban Turkiyya da ya fi ziyartar Afirka daga wajen nahiyar. Ziyarar da ya kai ta karshe zuwa Afirka ita ce ta watan Fabrairu, inda ya je kasashe uku – Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Senegal da Guinea-Bissau.

A watan Maris na 2016, watanni kadan kafin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da ‘yan ta’addar FETO suka yi, Shugaba Erdogan ya ziyarci Equitorial Guinea, Ghana da Nijeriya.

A watan Mayun wannan shekarar ya jagoranci tawagar ‘yan kasuwa da jami’an diflomasiyyar Turkiyya zuwa kasashen Afirka uku – Uganda, Kenya da Somalia. Ziyarar ta mayar da hankali kan fadada kasuwanci tsakanin bangarorin biyu da yaki da ‘yan ta’addar FETO da karfafa alakar diflomasiyya.

Daga 2003 zuwa yau, Shugaba Erdogan ya ziyarci sama da kasashen Afirka 30. Hoto: AA

Daga shekarar 2003 zuwa yau, shugaba Erdogan ya ziyarci sama da kasashen Afirka 30. A dukkan wadannan ziyara, an dinga sanya hannu kan yarjeniyoyin hada kai da zuba jari.

An gudanar da tarukar ganawar ‘yan kasuwa daga bangarorin biyu. Kamfanunnukan Turkiyya da na Afirka sun hadu da juna tare da neman hanyoyi mafiya kyau da su hada kai waje guda.

Inganta masana’antar tsaro

A ‘yan shekarun nan, Shugaba Erdogan ya kara kaimi wajen ganin Turkiyya ta tsaya da kakafunta a bangaren tsaro, ba tare da neman taimako daga waje ba.

Wannan kokari abin yabawa, ya bayar da gudunmawa wajen habakar masana’antar kayan tsaro ta Turkiyya, wadda a yanzu na daya daga cikin jagorori a duniya wajen samar da kayan tsaro na zamani.

Jami’an tsaron Turkiyya na amfani da kayan tsaron da aka samar a cikin gida wajen fatattakar ‘yan ta’adda na PKK/YPG a arewacin Siriya da Iraki.

Bayan samar da kayan aiki ga jami’an tsaron Turkiyya, masana’antar tsaron kasar na sayar da kayan ga kasashen waje.

A baya-bayan nan an ga irin rawar da jiragen yaki marasa matuki na Turkiyya samfurin Bayraktar TB2 suka taka a Yukren don kalubalantar Rasha. A Karabakh, Azabaijan ta yi amfani da Bayraktar TB2 don fatattakar mayakan Armeniya da suka mamayi iyakarta.

Jiragen yaki marasa matuki na Turkiyya sun kuma taimaki kasashen Afirka da dama da suka hada da Libiya da Burkina Faso wajen yaki da ta’addanci.

Za a iya cewa a yanzu Turkiyya na dab da zama mai cin gashin kanta dari bisa dari wajen samar da kayan tsaro sakamakon jajircewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Kasashen Afirka na kan gaba wajen sayen kayan tsaro daga Turkiyya.

Turkiyya ta sanya hannu kan yarjeniyoyin sayar da kayan tsaro da kasashen Afirka sama da 30. Hoto: AA

Sama da kasashen Afirka 30 da suka hada da Nijeriya, Benin, Chad, Congo, Djobouti, Gabon, Gambia, Ginea-Bissau, Ivory Coast, kenya, Libiya, Mali, Nijar, Sanagal, Tanzania, Rwanda, Ghana, Madagascar, Sudan, Somalia, Tnusia da Uganda sun sanya hannu da Turkiyya don sayen kayan tsaro.

A yanzu haka, wasu jami’an tsaron sojin saman Nijeriya na samun horo a Ankara kan yadda ake sarrafa jirgin saman yaki mai saukar ungulu samfurin T-129 da Nijeriya ta saya daga kamfanin TUSAS na Turkiyya.

A 2022, Nijeriya ta sanar da sayen jiragen yaki masu saukar ungulu samfurin T-129 guda shida daga TUSAS, a wani bangare na kokarin kakkabe ta’addanci daga iyakokinta.

Diflomasiyya da safarar jiragen sama

Turkiyya ce kasar da ta fi kowacce kasa a duniya yawan ofisoshin jakadanci a Afirka da ke wajen nahiyar. Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana cewa ya zuwa yanzu kasar na da ofisoshin jakadanci 44 a nahiyar Afirka.

Farfesa Turhan ya alakanta wannan ci-gaba da dauwamar hadin kai da ke amfanar bangarorin biyu, da yawaitar ziyartar nahiyar da Shugaba Erdogan ke yi, da kuma zuwa Turkiyya da shugabannin Afirka ke yi bayan abin da ya faru a daren 15 ga Yulin 2016.

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya kara yawan wuraren da yake ziyarta a Afirka, inda ya zama jirgin saman wajen Afirka da ya fi kowanne zuwa biranen Afirka.

Ya zuwa watan Mayun 2023, kamfanin jiragen saman Turkiyya na zuwa birane 66 a kasashen Afirka 44.

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya kara yawan kasashen da yake zuwa a kasashen Afirka 61 zuwa 62. Hoto: AA

Karantarwa da tallafin karatu

Turkiyya ta bayar da muhimmanci ga manufofinta na hadin kai da Afirka.

Farfesa Turhan ya ce bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga Yulin 2016, Turkiyya ta mayar da hankali kan manufofin ginawa da ma samar da ci-gaba a Afirka.

Ya shaida wa TRT Afrika cewa “A kokarin da take na kassara ayyukan FETO a wajen kasar bayan kakkabe su a cikin gida, Turkiyya ta fara sabon shiri da ya bayyana Afirka a matsayin babbar kawa.”

“FETO na gudanar da ayyuka a Afirka, kuma Turkiyya ta fara kokarin dakatar da ayyukan kungiyar ta’addanci a duniya baki daya.

Wannan na nufin mayar da hankali kan kungiyoyin farar-hula da makarantun kungiyar, wadanda suka zama hanyar kamun-kafa da neman wajen shigar kungiyar a kasashe da dama.

Kungiyar ta’addar ta dinga yada farfaganda game da Turkiyya ta kowacce hanya da ta samu dama. Hakan ya sa Shugaba Erdogan, a duk lokacin da ya hadu da shugabannin Afirka, yake kokarin jan hankalinsu kan hatsarin kungiyar FETO.”

A lokacin da Shugaba Erdogan ya ziyarci wasu kasashen Kudanci da Gabashin Afirka irin su Tanzania, Mozambique da Madagascar, ya mayar da hankali wajen fito da barazanar da FETO ke yi wa Afirka.

Farfesa Turhan na ganin cewa Turkiyya na daukar matakai hudu don fatattakar FETO daga Afirka.

Na farko kuma mafi muhimmanci shi ne bunkasa ilimi, wanda shi ne bangaren da ya fi tara wa ‘yan ta’addar FETO kudi daga kasashen Afirka.

A watan Yunin 2016, Turkiyya ta kafa Gidauniyar Maarif don gudanar da ayyuka a ciki da wajen Turkiyya. Aikin Gidauniyar shi ne ya karbe ragamar dukkan makarantun FETO da ke kasashen duniya da suka hada da na Afirka.

Shugaban Gidauniyar Maarif Farfesa Birol Akgun ya shaida wa TRT Afirka cewa a yanzu haka suna gudanar da ayyuka a kasashen Afirka 25.

“Kasashe 15 daga cikinsu sun mika wa Gidauniyar Maarif makarantun da FETO ke kula da su," in ji shi.

Gidauniyar Maarif ta yi nasara wajen karbe wasu makarantun FETO a kasashen Afirka da suka hada da Tanzania. Hoto: AA

Gidauniyar Maarif na karbe wadannan makarantu ne don kubutar da kasashen Afirka daga hatsarin da FETO ke da shi, sannan a toshe dukkan hanyoyin da kungiyar ke tara kudade.

A lokacin da Afirka ta zama dandalin gasar kasashen duniya, Turkiyya na bukatar kara kaimi don samun matsayin da ya cancance ta a nahiyar.

Akwai bukatar kara yawan jari na kai-tsaye a Afirka daga Turkiyya, musamman a bangarorin noma, makamashi, gine-gine, tsaro da ilimi.

TRT Afrika