An harba kumbon da kasar Turkiyya ta kera zuwa sararin samaniya, kamar yadda hukumar masana’antu da tsaro ta kasar SSB ta tabbatar.
Kumbon, wanda kamfanin ROKETSAN ya kera, an yi gwajinsa ne a arewa maso yammacin lardin Kirklareli a ranar Asabar, in ji SSB a shafinsa na X, wanda a baya aka fi sani da Twitter.
“Kumbonmu na bincike, wanda aka hada shi da fasaharmu ta aikin injiniya ta zamani a matakin kasarmu na zuwa sararin samaniya, an harba shi daga Igneada,” in ji SSB.
Ministan masana’antu da fasaha Mehmet Fatih Kacir shi ma ya yaba da kaddamar da kumbon da aka yi tare da taya murna ga ROKETSAN.
Kamfanin na ROKETSAN, wanda aka kirkiro a 1988 bayan amincewar kwamitin tsaro na kasar, “na da burin zama kan gaba ta fannin tsaro a duniya” ta hanyar samar da kayayyaki na cikin gida da suka hada da kumbo da rokoki.
Haluk Gorgun, wanda shi ne shugaban masana’antun tsaro na Turkiyya, ya bayyana cewa “nazarin sararin samaniya na Turkiyya zai kara habaka,” sakamakon sabuwar fasahar ta kumbon.